Alkawarin Aure: An Fara Gabatar da Shaidu Kan Hadiza Gabon a Kotun Shari'ar Musulunci

Alkawarin Aure: An Fara Gabatar da Shaidu Kan Hadiza Gabon a Kotun Shari'ar Musulunci

  • Ana ci gaba da shari'ar jarumar Kannywood, Hadiza Gabon da wani ma'aikacin gwamnati Bala Musa wanda ke tuhumarta da ci masa kudi tare da kin aurensa
  • Wani shaida mai suna Shamsudeen Mohammad wanda abokin aikin Musa ne yace da idonsa ya ga jarumar a lokacin da suke kiran bidiyo da masoyin nata
  • Sai dai ya ce a takaice ya ganta domin an samu matsalar daukewar sabis inda suka koma yin magana ta waya

Kaduna - Wani shaida a shari’ar da ke gudana tsakanin Bala Musa da jarumar Kannywood, Hadiza Aliyu Gabon, ya fadama kotun Shari’a da ke zama a Kaduna cewa ya san lokacin da Musa ya yi kiran bidiyo da jarumar.

Shaidan mai suna Shamsudeen Mohammad, daga Samaru Gusau, jihar Zamfara, ya ce Musa, wanda abokin aikinsa, yana kiran jarumar a kan wayar, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Hauhawar Farashin Kaya: Gwamnatin Buhari Na Shirin Karawa Ma’aikata Albashi

A tuna cewa Musa, wanda yake ma’aikacin gwamnati ya yi karar shahararriyar jarumar a gaban kotu kan kin aurensa bayan ya kashe mata kudi N396,000.

Hadiza Gabon
Da Idona Naga Hadiza Gabon Lokacin Da Masoyinta Ya Kirata Ta Bidiyo, Shaida Ya Sanar Da Kotu Hoto: @adizatou
Asali: Instagram

Ya yi bayanin cewa sun hadu ne a Facebook kuma cewa tun lokacin suka kulla alaka da alkawarin aure.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Amma jarumar, a daya daga cikin bayyanar da tayi a gaban kotu, ta karyata batun saninsa, tana mai cewa bata taba haduwa da shi ba.

A halin da ake ciki, Shamsudeen, wanda aka gabatar a kotu a ranar Talata daga jihar Zamfara don bayar da shaida, ya fadama kotu cewa:

“Muna tare a ofis lokacin da shi (Bala) ya kirata ta kiran bidiyo. Na ganta a cikin bidiyon a takaice kafin sabis din watan ya samu matsala sannan suka koma kiran waya kawai. Harma ya aike mata da katin waya. Koda dai ban ji abun da suka tattauna ba, amma dai na san suna soyayya.”

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Wata cuta ta kama kama Nnamdi Kanu a hannun DSS, inji lauyansa

Bayan ya bada shaida, lauyan wacce ake kara, Barista Mubarak Sani Jibril, ya tanbaye shi ko ya ga Hadiza a yayin kiran bidiyon sai Shamsudeen ya ce ya kanta a takaice kafin sabis ya dauke.

Kan ko abokinsa Bala ya taba gabatar dashi ga jarumar a kan waya, shaidan yace a’a.

Lauyan mai kara, Barista Naira Murtala, ya fadama kotu cewa sauran shaidunsu za su zo daga Zamfara don haka ya roki kotu da ya rubuta wasika zuwa ofishinsu don a basu izinin zuwa da bayar da shaida, bukatar da kotu ta amince da shi.

Khadi na kotun, Rilwanu Kyaudai, ya umurci lauyoyin bangarorin biyu da su sanar da kotun ranar da suke so a ci gaba da zama sannan ya dage zaman.

Kannywood: Rayuwata Na Cikin Hatsari, Hadiza Gabon Ta Faɗa Wa Kotu

A baya, mun ji cewa jarumar Kannywood, Hadiza Aliyu Gabon, ta faɗa wa Kotun shari'ar Musulunci da ke Kaduna cewa rayuwarta na cikin haɗari.

Kara karanta wannan

Aika-Aikar Dan China: Gwamnatina Za Ta Dauki Mataki Kan Makashin Ummita, Inji Ganduje

Daily Trust ta rahoto cewa wani Bala Musa ya kai ƙarar Jarumar ne bisa zargin ta ƙi aurensa bayan kashe mata kuɗi N396,000.

A baya Gabon ta musanta cewa bata san mutumin ba. Alƙalin Kotun ya ɗage zaman daga 28 ga watan Yuni, 2022 zuwa 1 ga watan Agusta saboda rashin lafiyar matarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel