Yadda matashi ya rafke matar aure da tabarya, ya halakata a gaban yaranta a Kano

Yadda matashi ya rafke matar aure da tabarya, ya halakata a gaban yaranta a Kano

  • Kakakin rundunar yan sandan jihar Kano, Abdullahi Kiyawa ya tabbatar da kisan wata matar aure a kwatas din Danbare da ke Kano
  • Bincike ya nuna cewa, wani matashi mai shekaru 18 mai suna Abdulsamad Suleiman ne ya halaka ta da tabarya har cikin gidanta tare da raunata yaranta 2
  • Ya kai mata ziyara a matsayinsa na dan uwanta kuma ya sace wayoyi 3, ganin ta fahimci shi ya kwashe wayoyin yasa ya dauka tabarya ya buga mata a kai har rai yayi halinsa

Kano - Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama wasu matasa biyu da ake zargi da kashe wata matar aure a unguwar Danbare da ke cikin birnin Kano.

Matar gidan mai suna Rukayya Jamilu, mai shekaru 21, an kashe ta ne lokacin da maharan suka shiga gidanta suka buga mata tabaraya, sannan suka bar ‘ya’yanta biyu da munanan raunuka.

Kara karanta wannan

Alkali ya iza keyar magidancin Bakano gidan yarin kan satar Maggi

Yadda matashi ya rafke matar aure da tabarya, ya halakata a gaban yaranta a Kano
Yadda matashi ya rafke matar aure da tabarya, ya halakata a gaban yaranta a Kano. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya shaida wa Daily Trust da yammacin Laraba cewa, binciken da ‘yan sandan suka gudanar ya sa aka kama matashin mai suna Abdulsamad Suleiman mai shekaru 18 a unguwar Dorayi Chiranchi Quarters da ke karamar Hukumar Gwale ta Kano tare da wani da ake zarginsa da laifin mai suna Mu’azzam Lawan, mai shekaru 17, na wannan adireshin.

Kiyawa ya bayyana cewa mijin mamacin ya kai kara hukumar ‘yan sanda a ranar 12 ga watan Fabrairu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An ruwaito cewa, ya ce a lokacin da ya dawo daga wurin aiki, ya samu matarsa ​​a cikin jini a kan gadonta, da kuma ‘ya’yansa masu shekaru uku da daya da suka samu munanan raunuka.

Ya ce an gudanar da bincike ne daga sashen binciken manyan laifuka na rundunar ‘yan sandan da kuma hukumar DSS na jihar wanda ya kai ga kama Suleiman.

Kara karanta wannan

Daukar fansa: Fusatattun matasa sun far wa matafiya a wani yankin Kaduna

“A bisa bincike mai tsanani, babban wanda ake zargin ya amsa cewa, a ranar 12/02/2022 da misalin karfe 16:00, ya je gidan marigayiya a matsayin dan uwanta, ya same ta a kan gado. Bayan ya gaisa sai ya ga wayoyi guda uku (3) kuma ya dauka.
“Bayan ya gane cewa ta gane shi, sai ya yi amfani da wata tabarya da aka kera ya buga mata kai, sannan ya bugi ‘ya’yanta guda biyu ya tafi da wayoyin hannu.
“Ya kuma kara da cewa, ya baiwa abokin nasa daya daga cikin wayoyin hannu, ya kuma sayar da sauran biyun akan Naira Dubu Sha Biyu (N12,000:00). An kama abokin nasa wanda ya amsa laifin sayar da wayar da aka ba shi na marigayiyar a kan Naira Dubu Biyu (N2,000:00),” Kiyawa yace.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Kiyawa ya kara da cewa za a gurfanar da shi gaban kotu idan an kammala bincike.

Kara karanta wannan

Abba Kyari shekaru 47 a duniya: Abubuwa 5 da baku sani ba game rayuwar Kyari

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Sama’ila Shu’aibu Dikko, ya yi gargadin cewa masu aikata laifuka ba za su samu mafaka a jihar Kano ba.

Innalillahi: An rasa rai 1 yayin da tankar mai ta yi arangama da tirela a Kano

A wani labari na daban, mutum daya ya rasa rayuwarsa bayan wata motar tirela ta kamfanin Julius Berger Construction ta yi karo da wata tankar mai na kamfanin mai na Mege a garin Chiromawa da ke kan hanyar Zaria a Kano.

Daily Trust ta ruwaito cewa, lamarin da ya kai ga barkewar gobara da ta lakume motocin biyu, ta kama da wani direban kamfanin Julius Berger mai shekaru 40, mai suna Aminu Dakatsalle, wanda aka ceto shi a sume kuma daga bisani aka tabbatar da mutuwarsa.

A yayin tabbatar da faruwar lamarin, Kakakin Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Yusuf Abdullahi, ya ce tankar man da ke dauke da litar man PMS (man fetur) kimanin lita 60,000 ta lalace a kan hanyar Zariya.

Kara karanta wannan

Kano: NSCDC Ta Kama Wani Mutum Da Katin Waya 22 Da Katin ATM 14

Asali: Legit.ng

Online view pixel