Tamfatsetsiyar sarkar miliyan 11 Hafsat Idris ta saka a sunan jikar ta

Tamfatsetsiyar sarkar miliyan 11 Hafsat Idris ta saka a sunan jikar ta

  • A kwanaki kadan da suka wuce ne aka girgije tare da shan shagalin sunan jikar jaruma Hafsat Idris inda jaririyar ta ci sunan kakarta
  • A wurin bikin, Hafsat Barauniya ta saka wani tsadadden leshi da wata tamfatsetsiyar sarkar gwal wacce ta kai naira miliyan 11
  • Shafin Labaran Kannywood ya bayyana kudin sarkar jarumar tare da yi mata fatan Allah ya kara arziki kuma ya raya jikartsa Hafsat Junior

A kwanaki kadan da suka gabata ne aka yi sunan jikar Hafsat Idris inda jaririyar ta ci sunan Hafsat Junior.

Sai dai shagalin sunan ya dauka hankali matuka duba da yadda wani bikin auren bai kai shi tara jama'a da tsaruwa ba, musamman jaruman Kannywood mata da suka cika wurin kuma aka yi bushasha.

Kara karanta wannan

Ke duniya: Ɗa ya doke mahaifinsa da taɓarya, ya aike shi barzahu a jihar Yobe

Tamfatsetsiyar sarkar miliyan 11 Hafsat Idris ta saka a sunan jikar ta
Tamfatsetsiyar sarkar miliyan 11 Hafsat Idris ta saka a sunan jikar ta. Hoto daga @Hausafilmsnews
Asali: Twitter

Mahaifiyar mai jegon ta yi fitar kece raini inda ta saka wani tsadajjen leshi dan ubansu da sarkar gwal da aka yi kiyasin kudin ta ya kai naira miliyan 11.

Shafin Labaran Kannywood da ke dandalin sada zumunta na Twitter ne ya tabbatar da hakan inda ya wallafa hoton jarumar tare da rubuta:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Sarkar gwal din da jaruma Hafsat Idris ta saka ranar sunan jikarta Hafsat Junior an ce kudinta ya kai naira miliyan goma sha daya. Allah ya kara arziki, Allah kuma ya raya Hafsat karama, Amin."

Bidiyoyin jaruman Kannywood mata da Hafsat Idris inda suke girgijewa a sunan jikar ta

A wani labari na daban, jarumar Kannywood ta shirya kasaitacciyar liyafar shagalin bikin suna, bayan diyar ta da ta aurar a shekarar da ta gabata ta sunkota mata jika wacce aka yi mata takwara da ita.

Kara karanta wannan

Bidiyoyin jaruman Kannywood mata da Hafsat Idris inda suke girgijewa a sunan jikar ta

Jaruman Kannywood mata ba a bar su a baya ba, sun halarci sunan kwan su da kwarkwatarsu domin nuna kara da murna ga fitacciyar jarumar.

A bidiyoyin da Legit.ng ta tattaro a shafin Instagram na jaruma Hafsat Idris, an ga yadda jaruman mata suka dinga kwasar rawa cike da murna tare da nishadi yayin da suka halarci sunan.

Mahaifiyar mai jegon ta bayyana tare da kawayenta inda suka yi shiga ta kece raini tare da alfarma, an ci, an sha tare da girgijewa cike da nishadi inda ake taya ta sam barka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel