Tausasan kalaman soyayya da Ahmed Indimi ya zayyanowa Zarah Buhari ranar bazday din ta

Tausasan kalaman soyayya da Ahmed Indimi ya zayyanowa Zarah Buhari ranar bazday din ta

  • Ahmed Indimi, sirikin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya wallafa tausasan kalaman soyayya ga Zahra Buhari a ranar zagayowar haihuwar ta
  • Kamar yadda Ahmed Indimi ya ce ga matarsa, shakuwar da ke tsakaninsa da Zahra 'yar kwalisa ba a iya rabawa saboda karfin ta
  • Tuni jama'a suka fara tururuwa tare da taya diyar shugaban kasan murnar wannan babbar ranar a rayuwar ta

A ranar 18 ga watan Disamban 2021, Zarah Buhari Indimi ta samu karin shekara daya kan shekarun ta na haihuwa.

Mijin ta, Ahmed Indimi, ya garzaya shafinsa na Instagram da safiyar Asabar inda ya bayyana yadda ya ke ji game da 'yar kwalisar matarsa yayin zagayowar ranar haihuwar ta.

Tausasan kalaman soyayya da Ahmed Indimi ya zayyanowa Zarah Buhari ranar bazday din ta
Tausasan kalaman soyayya da Ahmed Indimi ya zayyanowa Zarah Buhari ranar bazday din ta. Hoto daga @thebeginningofyz
Asali: Instagram

Kamar yadda ya wallafa:

"Barka da ranar zagayowar haihuwar ki rai mai cike da abubuwan mamaki @mrs_zmbi.

Kara karanta wannan

Shugabannin kungiyar ASUU sun dauki matsaya a kan batun sake komawa yajin aiki a Najeriya

"Hadin da ke tsakanina da ke ba a iya musantawa, ba a iya kwatanta da yawan son da na ke miki, shakuwar da ke tsakaninmu da juna ba a iya raba ta. Barka da ranar zagayowar haihuwar ki masoyiya ta."

Babu bata lokaci jama'a suka garzaya tare da fara taya ta murnar zagayowar ranar haihuwar ta.

Martanin mutane

@eesha5043 cewa ta yi: "Barka da zagayowar ranar haihuwa. Ina fatan albarka da kariyar Allah ba za ta taba yankewa daga gare ki ba."
@roselinetasha kuwa tsokaci ta yi da: "Ina taya ki murnar zagayowar ranar haihuwar ki."
@rasheedatomolara1 ta ce: "Ina taya ki murnar zagayowar ranar haihuwar ki Zahra kyakyawa. Allah ya albarkaci sabuwar shekarar ki."
@emirate_kamalya ce: "Na taya ki murnar ranar zagayowar haihuwar ki. Barkan ku."

Kara karanta wannan

Sheikh Jingir ya magantu kan karuwar rashin tsaro, ya aike wa 'yan Najeriya muhimmin sako

@mercy_osaghai: "Barka da ranar zagayowar haihuwa ga kyakyawar matar ka. Ina fatan za ta kasance koyaushe cikin farin ciki."

Bana son warkewa daga wannan haukar: Ahmed Indimi ya rubuta kalaman soyayya ga matarsa Zahra Buhari

A wani labari na daban, surukin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Ahmed Indimi, ya birge mabiya a kafofin sada zumunta da irin rayuwar soyayyarsa bayan ya rubuta wa matarsa Zahra Buhari kalmomi masu dadi.

Da ya je shafinsa na Instagram, dan hamshakin dan kasuwa ya bayyana yadda yake haukan son matarsa.

Matashin ya wallafa hotonsa tare da Zahra inda ya raka shi da rubutu mai ratsa zuciya wanda ya kayatar da mabiya kafofin sada zumunta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel