Bana son warkewa daga wannan haukar: Ahmed Indimi ya rubuta kalaman soyayya ga matarsa Zahra Buhari

Bana son warkewa daga wannan haukar: Ahmed Indimi ya rubuta kalaman soyayya ga matarsa Zahra Buhari

  • Surukin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Ahmed Indimi, ya nunawa mabiyansa a yanar gizo cewa shi gwanin iya soyayya ne
  • Dan hamshakin attajirin ya wallafa hotonsa tare da matarsa, Zahra Buhari, sannan ya bi shi da kalamai masu dadi wanda ya birge mabiyansa
  • Matashin ya kuma rubuta a cikin bayaninsa cewa idan so hauka ne, ba ya burin sake samun lafiya

Surukin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Ahmed Indimi, ya birge mabiya a kafofin sada zumunta da irin rayuwar soyayyarsa bayan ya rubuta wa matarsa Zahra Buhari kalmomi masu dadi.

Da ya je shafinsa na Instagram, dan hamshakin dan kasuwa ya bayyana yadda yake haukan son matarsa.

Bana son warkewa daga wannan haukar: Ahmed Indimi ya rubuta kalaman soyayya ga matarsa Zahra Buhari
Ahmed Indimi ya rubuta kalaman soyayya ga matarsa Zahra Buhari Hoto: ahmed.indimi
Asali: Instagram

Matashin ya wallafa hotonsa tare da Zahra inda ya raka shi da rubutu mai ratsa zuciya wanda ya kayatar da mabiya kafofin sada zumunta.

Kara karanta wannan

Hotuna da bidiyoyin kasaitacciyar liyafar cin abinci dare ta bayan daurin auren Yusuf da Zahra

A cewar Ahmed, idan kasancewa cikin soyayya wani nau'in hauka ne, baya fatan ya sake samun hankali.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya rubuta:

"Kuma idan so hauka ne, kada Allah ya sa na sake samun natsuwa."

Kalli wallafarsa a kasa:

Ma’auratan sun birge 'yan Najeriya matuka

Yawancin masu amfani da intanet suna mamakin yadda Ahmed ke nuna soyayya don haka suke nuna sha’awarsu ga dangantakarsa da Zahra Buhari.

Ga martanin wasu daga cikinsu a kasa:

Bighstudios:

“Ikon Allah. Wanene zai yi amfani da irin wannan kalaman a kaida .. Allah sai yaushe.”

Soulunraveled:

“Awwwww. Allah ya kiyaye soyayyar ku kuma ya daidaita muku shi❤️. ”

Ochuatom:

"Ina kaunar yadda yake son ta, son matar ka karfi ne ba rauni ba."

Kyawawan hotunan zuka-zukan 'ya'yan Buhari mata da mazansu na aure

Kyawawan hotunan 'ya'ya matan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Halima, Zahra da Hanan tare da mazansu na aure yayin liyafar cin abincin rana ta bikin dan uwansu, Yusuf Muhammadu Buhari sun bayyana.

Kara karanta wannan

Ba zai yiwu in bar mulki a kunyace ba: Shugaba Muhammadu Buhari

An yi kasaitacciyar liyafar, wacce ta hada manyan mutane a ranar Lahadi, 22 ga watan Augusta a Banquet Hall dake fadar shugaban kasa ta Aso Villa.

'Ya'yan shugaban kasan mata sun karkace tare da daukar kyawawan hotuna da mazansu na aure yayin da ake liyafar cin abincin ranan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng

Online view pixel