Fim din Labarina: Baba 'Dan Audu ya bayar da sharadin daina damfara

Fim din Labarina: Baba 'Dan Audu ya bayar da sharadin daina damfara

  • Shiri mai dogon zango na Labarina ya dauko zafi inda aka ga Baba 'Dan Audu ya na zuba ruwan rashin tausayi da kuma kwadayi
  • Sai dai a taunawar da aka yi da Baba 'Dan Audu, ya bayyana cewa idan an gaji da ganin damfararsa, a tattara masa kudi ya koma Saudi
  • A shirin makon da ya gabata, an ga cewa jarumin Mahmud ya rasu, amma hakan bai sa Baba 'Dan Audu ya tausayawa wannan rashin ba

Bayan shirin Labarina mai dogon zango ya karade ko ina, Baba 'Dan Audu ya bayyana dalilansa na damfara tare da kwadayi a fim din.

Ya fito ne a matsayin Baba Dan Audu a cikin shirin inda aka nuna shi a matsayin mutum mai matukar kwadayi.

Read also

Kutsen gidan Odili: Malami da wanda ake zargi sun yi uwar watsi

Mutane da dama sun dinga cece-kuce a kan yadda yake bin har masu zuwa gaisuwar mutuwa ya na rokonsu bayan mutuwar dan matarsa (Mahmud).

Labarina: Baba 'Dan Audu ya bayar da sharadin daina damfara
Labarina: Baba 'Dan Audu ya bayar da sharadin daina damfara. Hoto daga BBC.com
Source: UGC

A wata tattaunawa da BBC Hausa ta yi da shi, ya bayar da hujjoji gamsassu wadanda suka janyo damfarar da ya ke yi a cikin fim din.

A cewarsa, koro shi daga Saudiyya ne ya yi sanadin wannan halayya ta shi, kuma ya dawo Najeriya babu ko sisi cike da fatara.

A cikin hirar, Baba Dan Audu ya kara da cewa:

“Ni abin nan ya na ba ni mamaki, mutane sai su ce Baba Dan Audu bai da mutunci. Ni ban san me suke so Baba Dan Audu ya yi ba. Sun kasa gane wane ne Baba Dan Audu. Kuma sun kasa gane halin da Baba Dan Audu ya ke ciki.

Read also

Jaruma Rahama MK, matar gwamna a fim din Kwana Casa'in ta yi auren sirri

“Idan da wani ne yake cikin halin da Baba Dan Audu ya ke ciki ina mai tabbatar maka zai iya fashi da makami, amma ka ga Baba Dan Audu saboda imanin sa, bai dauki kayan kowa ba.”

Ya ce ba duk mutum ba ne zai shiga irin talaucin da Baba Dan Audu ya shiga a raba shi da zamba cikin aminci da sauran su.

A cikin shirin Labarina na makon da ya gabata, an bayyana yadda Baba Dan Audu ya nuna zalamar sa a fili duk da mutuwar da aka yi wacce ta firgita kowa.

Yanzu haka kowa ya zuba ido ya na kallon yadda za ta kaya tsakanin sa da matar sa (Mahaifiyar Mahmud) da kuma Umar (Abokin Mahmud) a cikin shirin.

Source: Legit

Online view pixel