Sabbin hotunan Rahama Sadau da Hadiza Gabon sun janyo cece-kuce

Sabbin hotunan Rahama Sadau da Hadiza Gabon sun janyo cece-kuce

  • A kwanaki biyu da suka gabata, Rahama Sadau ta wallafa wasu zafafan hotunan ta sanye da bakar riga da takalmi fari
  • Jaruma Hadiza Gabon kuwa ta ziyarci birnin Newyork inda ta saka babban hijab tare da wallafa hotunan ta a Instagram
  • Babu shakka wadannan hotunan sun bar baya da kura tunda kuwa jama'a sun dinga sukar Rahama tare da yaba wa Hadiza Gabon

Sabbin hotunan jaruman Kannywood, Rahama Sadau da na Hadiza Aliyu Gabon sun janyo maganganu daban-daban a kafar sada zumuntar zamani ta Instagram.

A kwanaki biyu da suka gabata, jaruma Rahama Sadau ta wallafa wasu hotunan ta sanye da wata bakar riga wacce ke bayyana ilahirin surar jikin ta.

Kamar yadda ta wallafa a shafin ta mai suna @rahamasadau, ta saka hotunan tare da rubuta:

Read also

‘Yan bindiga sun saki ‘yan asalin jihar Benue da suka sace a Zamfara

"Ba za ka taba gajiya ba matukar ka na gwada sabbin abubuwa".
Sabbin hotunan Rahama Sadau da Hadiza Gabon sun janyo cece-kuce
Sabbin hotunan Rahama Sadau da Hadiza Gabon sun janyo cece-kuce. Hotuna da @adizatou, @rahamasadau
Source: Instagram

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jama'a sun yi martani

Babu shakka wadannan hotunan sun tada kura yayin da suka samu jinjiina ta sama da mutum dubu ashirin a cikin kwanaki biyu kacal. Ga wasu daga cikin martanin da aka yi mata:

Mai amfani da suna @ibrorabi ta ce: "Toh fah! Yanzu arewa za su yo caa a kan ki ko kuma hisbah".
Shi kuwa @herbeebu_haruna cewa yayi: "Tabbas ba za mu taba gundura ba matukar kina wallafa mana kyawawan hotunan ki".
@itz_muftahod cewa yayi: "Daga India an wuce China kenan. Su Rahama yawon bude ido".
@rikwende_kefas cewa yayi: "Toh fa... Da fatan Kano ba za su fatattako ki ba."
@_ummisani cewa tayi: "Wawuya".
@dan_isah91 ya ce: "Jahilci mugun ciwo".
@i_dr.yandoto cewa yayi: "Zai fi miki idan kika je kika yi aure kafin zuwan dujal. Ke Rahama, anya har yanzu kina Musulunci kuwa? Koyaushe ido rufe ki ke abubuwa, ke mace ce, lokacin ki kalilan ne."

Read also

Sabon hari: 'Yan bindiga sun kai hari masallaci, sun bindige masallata a jihar Neja

A daya bangaren kuwa, jaruma Hadiza Gabon ta kai ziyara birnin New York da ke Amurka inda ta dauka wasu hotuna sanye da hijab wanda ya janyo mata yabo da jinjina daga mabiyan ta da masoya.

Martanin jama'a kan hotunan Gabon

@dj_sadeeq5 cewa yayi: "Dube ta, ta na da matukar saukin kai da karamci".
@sir_mustafa9 cewa yayi: "Allah ya kara daukaka ki yaya Anty Adizatou".
@dan_isah91: "Kin burgeni wallahi. Wannan shiga ta Musulunci ce".
@abubukarbbello1 cewa yayi: "Allah ya tsare ki da tsarewar shi adizatou".

Maryam Booth ta sa an kwamushe matashin da ya yada labarin ta na neman miji

A wani labari na daban, Shahararriyar jarumar Kannywood, Maryam Booth, ta sa an cafke mata wani matashi da ta zarga da yada labarai na karya kan ta inda aka sa shi yin bidiyo domin neman afuwar ta da janye miyagun kalamansa.

A kwanakin baya, labarin cewa Maryam Booth ta koka da yadda ba a saka ta fina-finai tun bayan bayyana bidiyon tsiraicin ta ya bazu.

Read also

Yan bindiga sun kutsa kai wurin Ibada ana tsaka da bauta, Sun yi awon gaba da mutum 3

Kamar yadda kagaggen labarin ya bayyana, jarumar ta shiga damuwa kuma ta ce ta na neman miji ido rufe domin ta yi aure ta huta.

Source: Legit.ng

Online view pixel