Dalilin da yasa ba a damawa da Matan Arewa a fannin da ya shafi fasaha
- Wata kungiyar fasaha mai suna STEM ta bayyana cewa akwai karancin matan arewa a fannin fasaha
- Kungiyar ta bayyana wasu dalilai da suka zamto jigo na hana matan shiga fannin na fasaha
- Hakazalika kungiyar ta bada shararwarin da ya kamata a bi don karfafa mata a fannin fasaha
A cewar wasu masu yada ilimin Kimiyya, Fasaha, Injiniyanci da Lissafi (STEM), idan aka zo batun shiga STEM, alkaluman suna kan raguwa a Arewacin Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.
Masu ba da shawara na STEM sun ce wannan raguwar za a iya danganta shi da dalilai da yawa.
Aisha Amoka-Mohammed, mai nazarin shirin kuma mai yada shirin STEM ta lura cewa rashin tallafi na daya daga cikin manyan matsalolin da ke hana ci gaban STEM tsakanin mata a Arewacin Najeriya.
“Rashin tallafi, gaba daya akwai karancin tallafin kayan fasaha a arewa. Har yanzu ba mu rungumi fasahar kere kere a arewa sabanin bangaren kudancin Najeriya ba,” inji ta.
KU KARANTA: Bamu gayyaci Sunday Igboho ya ya taya mu korar Fulani ba, gwamnan jihar Ogun
"Wannan hade da 'yan matsalolin da suka shafi fasaha na hana matan shiga fasaha."
Mohammed Ibrahim Jega, wanda ya kafa kungiyar Startup Arewa ya bayyana wasu daga cikin abubuwan da suka hada da abubuwan da suka shafi muhalli, zamantakewa da addini.
Tsoron fasaha
Wanda ta kirkiri kamfanin Blue Hub Saphire, Maryam Lawan Gwadabe, ta bayyana cewa tsoron amfani da kayan fasaha ko tsunduma cikin ayyukan da suka shafi fasahar shima yana daya daga cikin abubuwan da ke iyakance shigar mata fasaha.
"Muna bukatar iyaye su tallafa wa 'ya'yaensu, kuma rashin mata abin koyi don karfafa tafiyar ta hanyar kirkirar hanyoyin da wasu za su bi shi ma wata dabara ce."
Me za ayi don cike wannan gurbi?
Don cike wannan gurbi, masu yada ilimin fasaha na STEM sun bada shawarar bin wadannan matakan:
Kirkirar dama: Karin damar da aka kirkira domin baiwa mata damar gogayya da abokan tsararrakinsu daga wasu sassan kasar.
Dama kamar ci gaban Kasuwanci, jagoranci, kasuwanci da kirkirar azuzuwan koyarwa don baiwa matan arewa fasahar kere kere.
Wayar da kai: Ya kamata a shirya shirin wayar da kai da sanar da daukar nauyin shirin karawa juna sani cikin al'umma a garuruwa daban-daban.
Haɓakawa: Nuna mata waɗanda suka yi nasarar karya shinge a cikin fasahar zamani don zama abin koyi. Hakanan wannan na iya haɗawa da sa hannun gwamnati, ƙungiyoyin addinai, da sauran masu ruwa da tsaki don taimakawa haɓaka tafiyar.
KU KARANTA: Gwamnatin Jihar Borno zata kafa kwalejin ilimin addinin Musulunci guda 27
Dama: Tunanin kirkiro da kuma nuna damar da mata zasu iya amfani da shi a cikin fasahar zamani.
STEM ta bayyana abubuwan da aka lissafa a matsayin abubuwan da zasu kawo nasara wajen sanya mata a fannin fasaha a arewacin Najeriya.
A wani labarin, Wasu mata a jihar Kaduna sun koka kan zargin sama-da-fadi da son kai a cikin tallafin N20,000 da ke gudana wanda Ma’aikatar Kula da Jin Kai ta Tarayya ke yi a jihar, The Guardian ta ruwaito.
Matan sun yi magana da Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a ranar Litinin a Kaduna a wurin da ake rabon kudin.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng