Gobara Ta Tilasta wa Jirgin Yakin Amurka Gudu wa daga Yakin Iran
- Jirgin ruwan yaki na Amurka USS Gerald R. Ford ya janye daga yankin Iran bayan ya samu matsala ana tsaka da kai wa Iran hari
- Rahotanni sun ce jirgin ya samu matsala bayan gobara ta tashi a cikinsa, ta jikkata ma’aikata biyu ba tare da lalata muhimman abubuwa
- Duk da haka, sauran jiragen rundunar na ci gaba da aiki a yankin Gabas ta Tsakiya yayain da Isra'ila da Amurka suka hada kai ana yakar Iran
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Gabas ta Tsakiya – Babban jirgin ruwan yakin rundunar sojin ruwan Amurka, USS Gerald R. Ford, ya bar ayyukan da yake yi a yankin da ake fama da rikici da Iran.
Rahotannin da aka fitar sun bayyana cewa jirgin ya janye daga fagen daga ne domin gudanar da gyare-gyare bayan wata gobara da ta tashi a cikin jirgin.

Source: Getty Images
Bloomberg ta wallafa cewa rahoton ya nuna cewa gobarar ta faru ne a ranar 12 ga watan Mari na shekarar 2026.
Jirgin yakin Amurka ya kama da wuta
MSSN a ta wallafa cewa duk da wutar ta kona wani sashe na jirgin, hukumomin sojin Amurka sun tabbatar da cewa ba ta da alaka da wani hari na yaki.
Duk da haka, ma’aikata biyu sun samu raunuka, amma an ce ba su cikin hadarin rasa rayuwa, kuma suna cikin koshin lafiya.
Wani jami’in Amurka ya bayyana cewa jirgin zai tsaya na dan lokaci a sansanin sojin ruwa da ke Souda Bay a tsibirin Crete domin tantance irin gyaran da za a iya yi masa.

Source: Facebook
Rahotanni sun kuma nuna cewa gobarar ta shafi wuraren kwanan ma’aikata, inda sama da gadaje 100 suka lalace.
Haka yayin gobarar, kusan ma’aikata 600 suka rasa wuraren kwana na wucin gadi saboda hayaki da ruwa da aka yi amfani da su wajen kashe wutar.
Tasirin janyewar jirgin yakin Amurka
Janyewar wannan jirgi mai muhimmanci ya zo ne a daidai lokacin da Amurka ke ci gaba da matsa lamba kan Iran, musamman dangane da barazanar da ake fuskanta a mashigar ruwa ta Hormuz.
Wannan jirgi ya kasance muhimmin dandali da jiragen saman yaki ke amfani da shi wajen kai hare-hare da kuma tsaron yankin.
Duk da janyewar USS Gerald R. Ford, sauran jiragen da ke karkashin rundunar “Carrier Strike Group” sun ci gaba da zama a yankin.
Daga cikin jiragen yakin akwai masu linzami irin su USS Mahan, USS Bainbridge da kuma USS Winston S. Churchill.
Babban hafsan hafsoshin sojin Amurka, Dan Caine, ya bayyana cewa suna fatan ma’aikatan da suka jikkata za su warke gaba tas.
An kuma bayyana cewa jirgin ya dade yana aikin sintiri tun daga watan Yunin 2025, inda ya fara a yankin Caribbean kafin daga bisani a tura shi Gabas ta Tsakiya.
Iran ta magantu kan harin Isra'ila
A baya mun wallafa cewa kasar Iran ta bayyana takaici game da halin ko-in-kula da Majalisar Dinkin Duniya ke nuna wa game da hare-haren da Amurka da Isra'ila ke kai mata.
Abin da ya fi ba ta takaici shi ne yadda ta yi zargin cewa Majalisar Dinkin Duniya da yin shiru kan kashe manyan jami’anta tun bayan da aka fara yakin a karshen Fabrairu.
Kasar ta ce shirun da aka yi na ƙarfafa Isra’ila wajen kai irin wadannan hare-hare, kuma kashe-kashen na iya zama ruwan dare a duniya
Asali: Legit.ng


