China Ta Shirya Kai Dauki, Ta Bayyana Tallafin da Za Ta Tura Kasar Musulunci Ta Iran
- Kasar China ta bayyana shirinta na kai wa mutanen Iran, Lebanon da wasu kasashen Gabas ta Tsakiya tallafin jin kai a wannan lokaci na yaki
- Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen China, Lin Jian ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai yau Talata
- China, wadda ake ganin tana da kyakkyawar alaka da Iran, ta sha yin kira ga Amurka da Isra’ila da su dakatar da hare-haren da suke kai wa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
China - Yayin da yakin Iran da Amurka/Isra'ila ke kara kamari, gwamnatin kasar China ta bayyana shirinta na kai dauki ga kasashen yankin Gabas ta Tsakiya da rikicin ya shafa.
China ta sanar a yau Talata cewa, za ta tura tallafin jin kai ga wasu kasashen Gabas ta Tsakiya, ciki har da Iran da Lebanon, wadanda hare-haren Amurka da Isra'ila suka shafa a yakin da ya shiga mako na uku.

Kara karanta wannan
"Ba mu miƙa wuya ga azzalumai": Iran ta gindaya sharadin kawo ƙarshen yaƙi da Amurka

Source: Getty Images
Tashar Al-Jazeera ta tattaro cewa sanarwar ta fito ne daga kakakin ma’aikatar harkokin wajen China, Lin Jian, yayin wani taron manema labarai a birnin Beijing.
Kasashen da China za ta tura tallafi
A cewar Lin Jian, gwamnatin China ta yanke shawarar bayar da tallafin gaggawa na jin kai ga kasashe hudu wadanda suka hada da Iran, Jordan, Lebanon da Iraq.
Ya ce tallafin zai taimaka wajen rage wahala da kuncin rayuwar da fararen hula ke ciki sakamakon yakin.
“China ta yanke shawarar bayar da tallafin gaggawa ga Iran, Jordan, Lebanon da Iraq. Muna fatan hakan zai taimaka wajen rage matsanancin halin da al’umma ke ciki,” in ji shi.
China ta kara kira da a kawo karshen yakin
China, wadda ake ganin tana da kyakkyawar alaka da Iran, ta sha yin kira ga Amurka da Isra’ila da su dakatar da hare-haren da suke kai wa Jamhuriyar Musulunci.
Sai dai Beijing ta kuma soki hare-haren da Iran ta kai kan wasu kasashen Tekun Fasha da ke dauke da sansanonin sojin Amurka, cewar rahoton China Daily.
Babban jami’in diflomasiyyar China, Wangi Yi, ya bayyana cewa, “wannan yaki bai kamata ya faru ba,” yana mai kira ga kasashen da su koma teburin tattaunawa.

Source: Getty Images
Kokarin da China take yi kan yakin Iran
China na kuma kokarin ba da gudummuwa wajen sasanta rikicin, inda wakilinta na musamman a Gabas ta Tsakiya, Zhai Jun, ya gana da ministan harkokin wajen Saudiyya domin tattauna hanyoyin dawo da zaman lafiya.
Sanarwar ta China ta zo ne bayan shugaban Amurka Donald Trump ya jinkirta ziyarar da zai kai Beijing, yayin da yake kara matsa wa China lamba ta taimaka wajen bude mashigar Strait of Hormuz.
Iran ta aika sako ga kasashen Musulmi
A wani rahoton, kun ji cewa babban jami’i a gwamnatin Iran, Ali Larijani, ya fitar da wani saƙo zuwa ga Musulmin duniya baki ɗaya da kuma gwamnatocin ƙasashen Musulmi.
Ali Larijani ya yi kiran hadin kai tare da sukar abin da ya bayyana a matsayin cin zarafi daga Amurka da Isra’ila a kan kasar Iran.
Jami’in na Iran ya kuma soki abin da ya bayyana a matsayin rashin nuna goyon baya daga yawancin ƙasashen Musulmi yayin wannan fafatawa.
Asali: Legit.ng
