Shirin Nukiliya: Iran Ta Gamu da Babbar Matsala a Yaƙin da Take Yi da Ƙasar Isra'ila

Shirin Nukiliya: Iran Ta Gamu da Babbar Matsala a Yaƙin da Take Yi da Ƙasar Isra'ila

  • Hukumar IAEA ta tabbatar da cewa Isra'ila ta lalata muhimman cibiyoyi biyu da Iran ke amfani da su a shirin mallakar makamin nukiliya
  • Wannan labari na zuwa ne yayin da rikicin Isra'ila da Iran ke ci gaba da tsananta tun ranar Juma'a ta makon jiya
  • Tun kwananin baya sojojin Isra'ila sun yi ikirarin lalata wurare biyu masu muhimmanci a shirin kera makamin nukiliyar Iran

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Iran - Rahotanni sun tabbatar da cewa Isra'ila ta lalata cibiyoyi da ƙasar Iran ke amfani da su a shirinta na ƙera makamin nukiliya a birnin Karaj, kusa da Tehran.

Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA) ce ta tabbatar da hakan yayin da yaƙi tsakanin Isra'ila da Iran ke ƙara ta'azzara.

An lalata muhimman wurare kera kayan nukiliya a Iran.
Isra'ila ta yi wa Iran illa mai girma a shirinta na ƙera makamin nukiliya Hoto: @IAEA
Source: Twitter

Hukumar IAEA ta bayyana lalata muhimman wuraren shirin nukiyar Iran ne a wata sanarwa da ta wallafa a shafin X yau Laraba, 18 ga watan Yuni, 2025.

Kara karanta wannan

A ƙarshe, Majalisar Dinkin Duniya ta tsoma baki kan rikicin Iran da Isra'ila

An lalata cibiyoyin shirin nukiliyar Iran

Ta ce cibiyoyin na dauke da masana’antun kera na'urori masu jujjuyawa, 'centrifuge' da Iran ke amfani da su a shirin nukiliyarta, a garin Karaj, kusa da babban birnin ƙasar, Tehran.

Sanarwar hukumar IAEA ta fito ne 'yan sa’o’i bayan da rundunar sojin Isra’ila ta tabbatar da kai hare-haren sama a yankunan da ke ciki da kuma kewaye da Tehran.

“IAEA ta samu labarin da ke nuna cewa an kai hari kan masana’antun kera kayan na'urar centrifuge guda biyu a Iran, watau cibiyar TESA da kuma Cibiyar Binciken Tehran," in ji sanarwar.

Hukumar ta ce duka wannan wurare biyu na karkashin kulawa da tantancewar IAEA ne a baya, bisa tsarin yarjejeniyar JCPOA da aka cimma da Iran a shekarar 2015 dangane da shirin nukiliyarta.

Iran ta gamu da matsala a shirin nukiliya

A wani hari daban da aka kai a wani wuri cikin birnin Tehran, IAEA ta ce:

Kara karanta wannan

Isra'ila: Iran ta umarci jama'a su daina amfani da whatsApp, ta fadi sharrin manhajar

“An kai hari kan wani gini da ake kera da kuma gwajin abubuwa da ke jujjuyawa na na'urar centrifuge.”
Yakin Isra'ila da Iran ya kara zafi.
Hukumar IAEA ta tabbatar da ikirarin sojojin Isra'ila na lalata cibiyoyin shirin nukiliyar Iran Hoto: Getty Image
Source: Getty Images

Tun kafin bayanin IAEA, rundunar sojin Isra’ila ta fitar da sanarwa cewa ta kai samamen sama a yankin Tehran domin dakile ci gaban shirin makamashin nukiliyar Iran.

“A cikin kokarin da ake yi na dakile shirin Iran na kera makamin nukiliya, an kai hari kan wani masana’antar kera na'urar centrifuge da ke Tehran,” in ji sojin Isra’ila.

Wannan na'ura na da matuƙar muhimmanci a tsarin tace Uranium, wanda shi ne abu mai matuƙar sarkakiya da ake amfani da shi wajen samar da man tashar makamashi ta nukiliya.

Yahudawa sun fara guduwa a Isra'ila

A wani labarin, kun ji cewa hare-haren da Iran ke ci gaba da kai wa ƙasar Isra'ila sun fara tilastawa yahudawa guduwa daga gidajensu.

Rahotanni sun nuna cewa ƴan kasar Isra'ila sun fara zama ƴan gudun hijira a wurare daban-daban bayan sun baro gidajensu.

Wannan na zuwa ne awanni bayan ƙasar Iran ta ƙara tabbatar da cewa ta harba jerin makamai masu linzami da jirage marasa matuka kan Isra'ila.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262