Ta tabbata, Nijar Ta Yi Watsi da Faransanci, Ta Zabi Hausa a Matsayin Harshen Ƙasa
- Gwamnatin sojan Nijar ta ayyana Hausa a matsayin harshen kasa, tare da cire Faransanci wanda ya samo asali daga mulkin mallaka
- Hausa ta riga ta zama gama gari a Nijar, musamman a Zinder, Maradi da Tahoua, yayin da kashi 13% kacal ke jin harshen Faransanci
- Nijar ta fice daga tasirin Faransa, ta kori sojojinta, ta canja sunayen tituna, tare da shiga sahun su Mali wajen ficewa daga Francophonie
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Nijar - A wani sabon sauyi da aka samu, gwamnatin mulkin soja ta Jamhuriyar Nijar ta ayyana Hausa a matsayin harshen da za a yi amfani da shi a ƙasar.
Wannan sabo kuma babban mataki da kasar ta dauka na nufin cewa ta cire harshen mallaka na Faransanci a matsayin harshen kasa na Nijar.

Asali: Twitter
Nijar ta mayar da Hausa harshen kasa
Wannan sauyi ya fito ne a cikin wani sabon kundin tsarin mulki da Nijar ta fitar a ranar 31 ga Maris, a cikin mujallar gwamnati ta musamman, inji rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar sanarwar gwamnatin, “Harshe na kasa shi ne Hausa,” yayin da “harsunan aiki su ne Turanci da Faransanci.”
An bayyana cewa Hausa ne harshen da mafi yawan mutane ke amfani da shi a fadin kasar, musamman a yankunan Zinder, Maradi da Tahoua.
An ce da yawan ‘yan Nijar da adadinsu ya kai miliyan 26 suna ji kuma suna magana da Hausa, yayin da kimanin miliyan uku kawai (kashi 13%) ke jin Faransanci.
An amince sojoji su ci gaba da mulki a Nijar
Sabon kundin tsarin mulkin ya kuma lissafa wasu harsunan gida guda tara, ciki har da Zarma-Songhay, Fulfude, Kanuri, Gourmanche da Larabci, a matsayin “harsunan magana na Nijar.”
Wannan sauyin harshe ya biyo bayan taron kasa da aka gudanar a watan Fabrairu, amma rahoton BBC Hausa ya nuna cewa ba kowa ke maraba da sauyin ba a Nijar.
Sai dai, wani rahoton ya ce gwamnatin sojan Nijar ta samu karin goyon bayan jama’a, kuma an amince wa Janar Abdourahamane Tiani da ya ci gaba da mulki har na tsawon shekaru biyar masu zuwa.
Yadda Nijar ta yanke alaka da kasar Faransa
Tun bayan juyin mulkin da ya kifar da shugaban farar hula Mohamed Bazoum a watan Yulin 2023, gwamnatin soja ta fara yanke alaka da kasar Faransa.
Matakan da aka dauka sun hada da korar sojojin Faransa daga Nijar, katse hulda da jakadanci da kuma sauya sunayen tituna da gine-ginen da ke dauke da sunayen Faransanci.
Kamar yadda Nijar ke kokarin kawar da tasirin Faransa, sauran kasashen da ke karkashin mulkin soja irinsu Mali da Burkina Faso suma suna bin irin wannan tafarki.
Kasashen uku sun fice daga kungiya ta Francophonie, wacce ke dauke da irin rawar da Commonwealth ke takawa ga kasashen da ke amfani da Ingilishi.
Asali: Legit.ng