Elon Musk Ya Dauko Sabon Gyara a Twitter, Zai Hana Mutane Yanke Alaka da Juna da Toshe Juna

Elon Musk Ya Dauko Sabon Gyara a Twitter, Zai Hana Mutane Yanke Alaka da Juna da Toshe Juna

  • Attajiri Elon Musk ya ci gaba da yin sauye-sauye ga kafar sadarwa ta X, wanda aka fi sani da Twitter a baya
  • Sabbin sauye-sauyen, idan aka aiwatar, za su hana miliyoyin masu amfani da kafar toshe juna da yanke alaka da juna
  • Elon Musk ya canza sunan dandalin sada zumunta na Twitter zuwa X 'yan watanni bayan ya sayi kamfanin akan dala biliyan 44

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Elon Musk, mamallaki kuma babban jami'in gudanarwa na X (wanda aka fi sani da Twitter), yana so ya hana masu amfani da kafar toshe juna da yanke alaka da juna a kafar.

Tsarin toshe juna na hana mutane sanin abin da ke faruwa a sashen juna, kana ba za su iya bibiyar juna a kafar.

Sai dai, a cikin sakon da ya fitar a dandamalinsa na X, Musk ya ce fasalin yanke alaka da juna bai da wata ma'ana kuma nan ba da jimawa ba zai kasance tarihi.

Kara karanta wannan

Arziki nufin Allah ne: Mutumin da ya zauna a Kanada tsawon shekaru 20, ya dawo ba nauyi

Elon Musk zai kawo sabon sauyi a Twitter
Za a haa toshe juna a Twitter | Hoto: @elonmusk
Asali: Facebook

Ya kuma bayyana cewa, a fannin tura sako ne kadai za a iya yanke alaka da juna duba da bukata da amfanin hakan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shawarar toshe Musk akan X

A cikin shekaru da yawa da suka shude, Musk ya kan yi alfahari da kansa a matsayin mai fafutukar 'yancin rofa albarkacin baki, dalili daya kenan da ya kai shi siyan dandamali a karshen 2022.

Kalubalen da zai fuskanta shine idan ya aiwatar da hana toshe juna, zai ci karo da zubin yarjejeniyar mahajoji na Apple da Google Play, inda ake sauyi manhajar X.

Apple yace, dole ne manhajojin da ke ba mutane mu’amala da juna su ba da kofar yanke alaka da juna da toshe juna.

‘Yan Twitter za su fara samun kudi

A wani labarin, Elon Musk, hamshakin attajirin da ya kafa kamfanin Tesla, ya ce ya sanya takunkumi ga adadin sakonnin da masu amfani da shafin Twitter za su iya karantawa a kullum.

Kara karanta wannan

Yadda Matasa Suka Babbaka Wani Mai Satar Yara a Arewacin Najeriya, Sun Ceto Mata 2 Da Ya Sace

A cewarsa, yunkurin zai yi aiki ne don magance batutuwan da suka shafi "tafiyar da bayanai da tsarin", kamar yadda ya bayyana shafinsa na Twitter a yau Asabar 1 ga watan Yuli.

Ya ce masu amfani da Twitter wadanda ke da assun da aka tantance sahihancinsu (verified) za su sami damar karanta rubutu 6,000 a kullum.

Asali: Legit.ng

Online view pixel