Shugaban Gambia Ya Dakatar da Tafiye-Tafiyen Kasashen Waje Ga Jami’an Gwamnati, Har da Shi Kansa

Shugaban Gambia Ya Dakatar da Tafiye-Tafiyen Kasashen Waje Ga Jami’an Gwamnati, Har da Shi Kansa

  • Ana ci gaba da fuskantar karyewar tattalin arziki a yankuna daban-daban na nahiyar Afrika da ma duniya baki daya
  • Kasar Gambia ta sanar da dakatar da tafiye-tafiye zuwa kasashen waje ga duk wasu manyan jami’an gwamnatin kasar
  • Rahoto ya bayyana dalilin da yasa aka yi wannan doka da kuma abin da ake son cimmawa don ci gaban kasar nan gaba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Gambia - Shugaban kasar Gambia Adama Barrow ya dakatar da duk wasu balaguro da jami'ai za su iya yi har da shi kansa domin rage kashe kudaden kasa, kamar yadda kakakin gwamnatin kasar ya sanar a ranar Asabar.

Barrow ya rattaba hannu kan dokar ne ga shi kansa, mataimakinsa, ministoci da manyan jami’an gwamnatin kasar.

A cewar rahoton daga Channels Tv da ke zuwa mana, wannan hani zai kasance na tsawon shekarar da ake ciki, inji sanarwar kakakinsa Ebrima Sankareh.

Kara karanta wannan

100 sun mutu: Yanzu haka 'yan Boko Haram da ISWAP suna can suna ta kwabza yaki a Borno

Shugaban Gambia ya hana tafiye-tafiye
An hana jami'an gwamnati tafiye-tafiye a Gambia | Hoto: foroyaa.net, un.org
Asali: UGC

Sai dai, tarukan da halartar ‘yan Gambia ta zama zama tilas da kuma tafiye-tafiyen kasashen waje ke daukar nauyinsu, wadannan za a iya zuwa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yanayin da Gambia ke ciki

Gambiya, kasa mafi kankantar nahiyar Afirka da ke da mazauna sama da miliyan biyu kacal, tana matsayi na 174 a cikin 191 a kididdigar ci gaban dan adam na Majalisar Dinkin Duniya, wanda ya hada da lafiya, ilimi da yanayin rayuwa.

Fiye da kashi biyar na al'ummar kasar na rayuwa ne a kasa da dala biyu a rana, a cewar bankin duniya. Hauhawar farashin kayayyaki a shekara ya kai 11.6% cikin dari a bara a kasar.

Kasancewar ana samun raguwar kudaden haraji, da kuma yawan tallafin da kasar ke bayarwa kan man fetur, taki da hatsi saboda illar yakin Ukraine, gibin kasafin kudin kasar ya kara fadada a bara, The Guardian ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Cin Hanci: Abba Gida Gida Ya Tsorata, Ya Bukaci Binciken Gaggawa A Kotun Sauraran Korafe-Korafen Zabe

Har ila yau, gibin kasafin kudi da kuma matakan basussuka sun karu, a daidai lokacin da kudaden haraji ke raguwa, kana ake kara zuba kudi karin tallafin man fetur, takin zamani da hatsi, sakamakon yakin Ukraine.

Allah ya dauke matamakin shugaban Gambia

A wani labarin, tataimakin shugaban kasar Gambia, Badara Joof, ya rigamu gidan gaskiya. Mai gidansa kuma shugaban kasar Gambia, Adama Barrow, ya bayyana cewa ya mutu ne bayan gajeruwar rashin lafiya.

Gabanin zama mataimakin shugaban kasa, Badara Joof, ya rike mukamin ministan kimiya da fasaha, bincike, da makarantun gaba da sakandare tsakanin 2017 - 2022.

Asali: Legit.ng

Online view pixel