Kasar Saudiyya Ta Rage Kudin Lasisin Kafa Gidajen Fim

Kasar Saudiyya Ta Rage Kudin Lasisin Kafa Gidajen Fim

  • Kasar Saudiyya ta sanar da ragi mai yawa a kan kudin lasisin kafawa da gudanar da harkokin gidajen fina-finai a fadin ƙasar
  • Ministan al'adun kasar ne yarima Badr bin Abdullah ya fitar da sanarwar tare da bayyana yadda sabon farsahin zai kasance
  • Ana sa ran ragin zai kawo saukin tiketin shiga gidajen fina-finai tare da inganta harkokin fim, musamman fina-finan kasar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Kasar Saudiyya ta sanar da rage lasisin mallaka da gudanar da gidan fim a fadin ƙasar. Sanarwar ta zo ne ta hannun ministan al'adu, Badr Abdullah.

Kasar Saudiyya
Kasar Saudiyya ta rage farashin mallakar gidajen fina-finai. Hoto: Muhammad bin Salman
Asali: Facebook

Ragin kudin ya shafi kudin bude gidajen fim din da kuma gudanar da gidajen fim na din-din-din da kuma na wucin gadi.

Kara karanta wannan

Hukumar FCCPC ta rufe kantin da ya hana 'yan Najeriya sayayya a Abuja

Ragin bude fim da aka yi a Saudiyya

A cewar jaridar Arab News, hukumar kula da fina-finai ta kasar ta sanar da cewa an rage kudin lasisin gidaje fim na dindindin a birane masu darajar A daga riyal 210,000 zuwa riyal 25,000

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A birane masu darajar B kuma ragin ya samu ne daga riyal 126,000 zuwa riyal 15,000. A birane ma su darajar C kuma saukin ya samu ne daga riyal 84,000 zuwa riyal 5,000

Ragin a kan gidajen fim na wucin gadi a birane masu darajar A ya kasance ne daga riyal 105,000 zuwa riyal 15,000

A birane ma su darajar B kuma daga riyal 63,000 zuwa riyal 10,000. A birane ma su darajar C kuma daga riyal 42,000 zuwa riyal 5,000.

Irin tasirin da ragin zai yi a Saudiyya

Kara karanta wannan

Sojoji sun gano gidan burodin 'yan ta'addan ISWAP a jihar Borno

Ana sa rai a kan cewa ragin zai kawo saukin tiketin shiga gidajen fim a fadin ƙasar kamar yadda jaridar Saudi Gazette ta ruwaito.

Wani shugaban gidan fim Abdullahi Al-Qahtani ya ce su na kokarin tattaunawa da ma su gidajen fim domin sauke farashin tiketi saboda sauƙin da aka samu.

Ya kuma kara da cewa suna duba yiwuwar saka fina-finan kasar Saudiyya a gidajen fim din domin cigaba da yada al'adun kasar.

An kara kudin zuwa kasar Saudiyya

A wani rahoton kuma, kun ji cewa Hukumar kula da Alhazai ta ƙasa (NAHCON) ta ƙara kuɗin zuwa aikin hajjin bana a ƙasar Saudiyya da Naira 1,918,032.91

Mai magana da yawun hukumar NAHCON, Fatima Sanda Usara, ta sanar da hakan, inda ta bayyana cewa hakan ya faru ne saboda tashin dala

Asali: Legit.ng

Online view pixel