Tsohon shugaban Gambia, Yahaya Jammeh ya koma gona
Tsohon shugaban kasar Gambia Yahaya Jammeh wanda a yanzu yake gudun hijira a kasar Equatorial Guinea ya rungumi harkar noma gadan gadan, inda aka hange shi a cikin gona.
Dama dai tun bayan komawarsa kasar Equatorial Guinea, Jammeh ya bayyana cewar shifa yanzu harkar noma zai koma ba kama hannun yaro, tunda dai Duniya tayi mai darasi.
KU KARANTA: Majalisar Dattawa za ta takawa irin su Hamid Ali burki
Kamar yadda rahoton jaridar BBC ya nuna, Jammeh ya kammala shirye shiryen fara harkar noman, sai dai ba’a tabbatar da wani irin noman zai shiga yi ba, amma dai hotunansa sun bayyana a cikin wata katuwar gona.
Idan ba’a manta ba, Jammeh ya tsere daga kasar Gambia ne bayan wani bore da yan kasa suka yi masa a daidai lokacin dayaki sauka daga mulki bayan ya sha kayi a zabukan kasar, duk da cewa ya kwashe shekaru 22 yana mulki.
Tserewar da yayi ne ya baiwa zababben shugaban kasar Adama Barrow daman darewa kujerar mulki, bayan kungiyar kasashen Afirka na yamma sun matsa ma Jammeh lamba.
Ga sauran hotunan:
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng