Mataimakin Shugaban Kasar Gambia, Badara Aliyu Joof, Ya Mutu A Ofis

Mataimakin Shugaban Kasar Gambia, Badara Aliyu Joof, Ya Mutu A Ofis

  • Shugaban kasar Gambia, Adama Barrowa ya sanar da mutuwar mataimakinsa
  • Barrow ya ce mataimakinsa ya mutu a kasar Indiya inda ya tafi jinya
  • Marigayin gabanin hawa kujerar mataimakin shugaban ya rike matsayin minista

Banjul - Mataimakin shugaban kasar Gambia, Badara Joof, ya rigamu gidan gaskiya.

Mai gidansa kuma shugaban kasar Gambia, Adama Barrow, ya bayyana cewa ya mutu ne bayan gajeruwar rashin lafiya.

Alieou Joof
Mataimakin Shugaban Kasar Gambia, Badara Aliyu Joof, Ya Mutu A Ofis Hoto: www.premiumtimesng.com
Asali: UGC

A jawabin da ya fitar a shafinsa na Tuwita, Adama Barrow, yace:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Ya ku yan kasar Gambia, da nauyin zuciya nike sanar muku rasuwar mataimakin shugaban kasa, Badara Alieu Joof."
"Ya rasu ne a kasar Indiya bayan gajeruwar rashin lafiya. Allah ya bashi Jannahtul Firdawsi,”

Gabanin zama mataimakin shugaban kasa, Badara Joof, ya rike mukamin ministan kimiya da fasaha, bincike, da makarantun gaba da sakandare tsakanin 2017 - 2022.

Kara karanta wannan

Hotunan Shugaba Buhari Inda Ya Samu Lambar Yabon Wanzar da Zaman Lafiya a Afrika

Asali: Legit.ng

Online view pixel