Morocco Ta Kasa Ta Farko da Ta Kai Wasan Kusa da Na Karshe a Kofin Duniya
- Ƙasar Morocco Ta Kafa tarihin zama ƙasa ta farko daga Nahiyar Afirka daga ta kai wasan dab da na ƙarshe a Kofin duniya
- 'Yan wasan sun kai wannan mataki ne bayan samun nasara kan Portugal da ci ɗaya mai ban haushi ranar Asabar
- Haka nan yan wasan sun zama larabawa na farko a tarihin Kofin duniya da suka taka wannan matsayi
Ƙasar Morocco ta kafa tarihin zama ƙasa ta farko daga nahiyar Afirka da ta kai wasan kusa da na ƙarshe (Semi Final) a gasar cin Kofin Duniya a Tarihi.
Channels tv ta tattaro cewa tawagar 'yan wasan Morocco sun kai ga nasara ne bayan Youssef En-Nesyri ya jefa kwallo a raga kafin zuwa hutun rabin lokaci a wasan da suka lallasa Portugal da ci ɗaya mai ban haushi.
Atlas Lions kamar yadda ake wa 'yan wasan laƙabi sun sake kafa tarihin zama Larabawa na farko da suka kai zagayen zakaru huɗu a wasan da ya gudana ranar Asabar a filin Al-Thumama, Qatar.
Ana ganin mai yuwuwa fitaccen ɗan wasan nan, Cristiano Ronaldo, ya buga wasansa na ƙarshe a gasar Kofin duniya bayan an sako shi a matsayin canji.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Sai duk da sako zaƙaƙurin ɗan wasan ya gaza jefa kwalllo a raga ta farko tun bayan fara wasannin kifa ɗaya kwala a gasar.
Morocco ta shiga gaban Portugal a Minti na 42 da fara wasan bayan ɗan wasa, Youssef En-Nesyri ya jefa kwallo da kai lokacin da suka farfaɗo da ƙarfi ana gab da tafiya hutun rabin lokaci.
Babu tantama ihun magoya baya ya ƙara wa 'yan wasan ƙasar arewacin Afirka karsashi duk da matsin lambar Portugal na ganin ta farke kwallo ɗayan, wannan shi ne karon farko da suka yi rashin nasara a Kwata Fainal.
Koci Fernando Santos ya sanya Ronaldo cikin wasan a farko-farkon dawowa daga hutun rabin lokaci amma mai rike da kambun Ballon D'Or guda 5 bai iya ceto zakarun kofin Uero 2016 ba.
'Yan wasan Koci Walid Regragui zasu barje gumi da ƙasar Ingila ko Faransa mai rike da kambun kofin a wasan zagayen kusa da na ƙarshe a Filin Al-Bayt ranar Laraba, rahoton Daily Trust ya tabbatar.
Morocco zata iya samun galaba kan kowace ƙasa daga cikin waɗannan ƙasashe ganin sau ɗaya kacal a ka jefa musu kwallo tun farkon gasar Kofin duniya 2022 a Qatar.
Asali: Legit.ng