Kungiyar Matasa A Arewa Ta Goyi Bayan Sabon Tsarin Babban Bankin Kasa kan Cire Kudi

Kungiyar Matasa A Arewa Ta Goyi Bayan Sabon Tsarin Babban Bankin Kasa kan Cire Kudi

  • Majalissar wakilai ta gayyaci gwamnan babban bankin kasa CBN, kan ya bayyana a gabatan a cikin makon da zamu shiga
  • Sanata Philip Aduda yace wannan tsari wani tsarine da bankin ya shigo da shi da zai takura talakawa
  • Wani masanin harkokin kuɗi Dr. Yusuf yace tauyewa ƴan Nigeria hakkinsu ne na ƙayyade musu kuɗin da zasu cire a banki

Abuja: ƙungiyar matasan tsakiyar Arewa mai suna "Middle Belt Youth Forum" sun goyi bayan sabon tsarin takaita fitar da kuɗaɗe na babban bankin Najeriya CBN.

Wannan na ɗaya daga cikin kudurorin wannan ƙungiya, kamar yadda suka bayyana a wani taron manema labarai da sukayi a Abuja, wanda jaridar Leadership ta ruwaito.

Godwin Meliga wanda yake shugaban ƙungiyar yace wannan tsarin zai magance ɓarna ga masu siyan kuri’u, masu aikata laifuka da suka shafi kudi da dai sauran laifuka wanda suke alaka da hakan.

Kara karanta wannan

Bidiyon Dake Yawo Na Shugaban APC Na Kasa Tsirara a Fadar Wani Babban Sarki a Arewa, Gaskiya Ta Fito

Babban Banki
Kungiyar Matasa A Arewa Ta Goyi Bayan Sabon Tsarin Babban Bankin Kasa kan Cire Kudi Hoto: Leadership
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya kuma bukaci duk ƴan Nijeriya masu son ganin Najeriya ta ci gaba da su goyi bayan wannan tsarin domin ita ce maslaha ga jama’a, ba kamar yadda wasu ke ganin an tsara tsarin ne ga iya wasu mutane ba.

A cewarsa, tsari ne mai kyau, ba wai anyi shi ne dan kara talautar da talakawan Najeriya ba, musamman ma wanda suke ganin shirin zai fi shafar Arewa.

Yace tsarin zai inganta tattalin arziki, tare da sa ido kan tassarufi da kuɗaɗe a bankuna da kuma kara inganta yanayin cinikayya a tsakanin Nigeria da sauran kasashe.

Sanarwar ta ci gaba da cewa,

“Muna farin cikin sanar da ‘yan Najeriya da abokan arziki cewa matasan Arewa sun amince da wannan sabon tsarin babban bankin kasa CBN.
“Ba mu da tantama cewa sabon tsarin zai ta taimaka wa al’ummar kasar wajen samun sahihin zabe da bunkasar tattalin arziki tare da taimaka wa yaki da cin hanci da rashawa.

Kara karanta wannan

Ku Maida Takardun Kudi Mara Fenti Bankuna, Gwamna Ya Bayyana Abinda Zai Faru Nan Gaba

Meliga ya ci gaba da cewa:

“Saboda haka muna kira ga ƴan Najeriya da su yi hattara da wadanda suka dukufa wajen ganin sun dakatar da manufofin don son kai.

Mai Yasa Kungiyar Ta Goyi bayan Dokar

Meliga ya ce ana ganin gazawar CBN na kula da kuɗaɗen kasar nan da kuma sune suka sabbaba jefa ƴan kasa cikin mawuyacin hali.

"Gwamnati ba za ta iya tsarawa da aiwatar da tsare-tsare ba tare da cikakken ikon sarrafa kuɗin da suke a babban bankin kaqsa ba, to dan haka dole ne bankin ya adana tare da tabbatar da kudin a cikisa domin juyashi," in ji shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel