Elon Musk, Jeff Bezos da Wasu Biloniyoyin Duniya 8 sun Tafka Asarar $50b a Rana Daya

Elon Musk, Jeff Bezos da Wasu Biloniyoyin Duniya 8 sun Tafka Asarar $50b a Rana Daya

  • Tabbas makon da ya gabata ya gigita manyan mashahuran masu arzikin duniya inda suka samu girgizar arziki
  • Elon Musk, Jeff Bezos da wasu manyan masu kudi takwas na duniya sun tafka asara a kamfanoninsu
  • Wadanda abin ya fi shafa su ne 'yan kasuwar fasaha wadanda suka kasa jajircewa karayar tattalin arzikin da duniya ke ciki

Manyan masu kudin duniya goma sun fuskanci girgizar tattalin arziki inda kan idanunsu $50 biliyan ta zama asara a dukiyarsu a ranar Talata, 13 ga watan Satumban 2022.

Babban mai kudin duniya, Elon Musk, ya tafka asarar $8 biliyan yayin da Tesla ta fadi da kashi 4 yayin da Jeff Bezos ya tafka asarar $10 biliyan saboda asarar kashi 7 da aka yi a Amazon kamar yadda rahoton Bloomberg ya bayyana.

Kara karanta wannan

Jerin Sunaye: Gwamna Ganduje Ya Ware biliyan N1.2 Don Ayyukan Hanyoyi 42

Elon Musk da Jeff Bezos
Elon Musk, Jeff Bezos da Wasu Biloniyoyin Duniya sun Tafka Asarar $50b a Rana Daya. Hoto daga Gareth Cattermole / Staff
Asali: Getty Images

Asarar ta fi shafar masu hannayen jari a fannin fasaha

Wadanda suke da kafanin Google, Larry Page da Sergey Brin kowannenus yayi asarar $5 biliyan kuma talla ta ragu a Google, wanda hakan ya kawo raguwar kashi 6 a hannayen jari.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

kamfanin Microsoft ya tafka asarar kashi 5 wanda ya kawo rashin $3 biliyan inda Bill Gates da Steve Ballmer suka rasa $5 biliyan kowannensu.

Jimillar arzikin Warren Buffet ya fadu da $3 biliyan. Kamfaninsa Berkshire Hathaway ya fadi kuma darajar Larry Ellison ta ragu inda ta koma $2 biliyan sakamakon faduwar hannyen jarin Oracle.

Mark Zuckerberg mai kamfanin Meta ya samu faduwar $6 biliyan sakamakon faduwar darajar hannayen jarin kamfaninsa.

'Dan kasuwar kayan karau kuma mamallakin LVMH, Bernard Arnault ya rasa dukiyarsa da ta kai $4 biliyan wanda yasa jimillar dukiyarsa ta kai $43 biliyan.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: 'Dan China Ya Sokawa Budurwarsa Mai Shekaru 23 Wuka a Kano, Ta Sheka Lahira

Wadanda suka fi tafka asara a cikinsu sune Bezos da Zuckerberg inda Bezos ya rasa $42 biliyan yayin da Zuckerberg ya rasa $68 biliyan.

Cikin Sa'o'i 8 Kacal, Dangote ya Tafka Asarar N9.42b, Arzikinsa Ya Koma Kamar na 2021

A wani labari na daban, hamshakin mai arzikin Afrika, Alhaji Aliko Dangote ya tafka asara inda dukiyarsa tayi kasa wanda bata taba yi ba a cikin watanni 12, kuma a halin yanzu dukiyarsa $18.8 biliyan ce cif.

Wannan ya faru ne bayan da $22.0 miliyan na dukiyarsa suka lalace a cikin kasuwanci cikin sa'o'i takwas kacal a ranar Laraba, 14 ga watan Satumban 2022.

Asali: Legit.ng

Online view pixel