Jerin Sunaye: Gwamna Ganduje Ya Ware biliyan N1.2 Don Ayyukan Hanyoyi 42

Jerin Sunaye: Gwamna Ganduje Ya Ware biliyan N1.2 Don Ayyukan Hanyoyi 42

  • Gwamnatin Abdullahi Ganduje ta ware kudi naira biliyan 1.2 don aikin hanyoyi 42 a cikin birnin Kano
  • Kwamishinan Labarai na jihar ya ce tuni aka kafa kwamitin da zai yi nazari kan lamarin harma an zabi wasu kamfanoni da za su yi aikin
  • Malam Muhammad Garba ya sake nanata kudirin gwamnatin Ganduje na samar da ababen more rayuwa don kyautata rayuwar al’ummar Kano

Kano - Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ware naira biliyan 1.2 don gina shataletale da gyaran hanyoyi 42 a cikin kuryar birnin Kano.

Kwamishinan labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi, 18 ga watan Satumba, a garin Kano, jaridar PM News ta rahoto..

Ya ce za a kashe kudaden ne kan aikin gina shataletale, gyara da kuma kula da hanyoyin da ke bukatar gyara sakamakon ambaliyar ruwa da rarake su.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa Ya Mance Da Batun Tinubu, Ya Fadi Wanda Zai Sa Ya Gaji Buhari Da Yana Da Iko

Ganduje
Jerin Sunaye: Gwamna Ganduje Ya Ware biliyan N1.2 Don Ayyukan Hanyoyi 42 Hoto: independent.ng
Asali: Twitter

Kwamishinan ya ce wasu daga cikin shataletalen da ake shirin gyarawa akwai na gidan mai na A A Rano da First Bank, da sauransu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kuma bayyana cewa an kafa kwamiti da suka hada da injiniyoyi na ma’aikatar ayyuka, hukumar tsare-tsare da ci gaba na jihar da kuma sauran ma’aikatu, sassa da hukumomi don su yi nazari kan lamarin don daukar matakin gaggawa.

Jaridar Punch ya rahoto cewa kwamishinan ya kuma ce tuni kwamitin ya tuntubi kamfanonin kwangila wanda an kwashi wasu don aiwatar da ayyukan.

Muhammad ya bayyana cewa an kebe wasu hanyoyi takwas don gyarawa da kula da su don tabbatar da zirga-zirgan ababen hawa cikin sauki.

Ayyukan sun hada da; FCE-Kofar Famfo Road, Gwarzo Road, Sheikh Jafar Road, Muhammadu Buhari Road, New Hospital Road, Sabo Bakin-Zuwo Road.

Sai kuma Lamido Crescent, Route to Cancer Treatment Centre, Dakata Road, DanHassa-Eastern Bypass, ‘Yan Mota-Kofar Mazugal Road, da Unguwar Abagana a yankin Fagge da ke birnin

Kara karanta wannan

Buhari ya magantu, ya ce akwai wadanda ya kamata suke tallata gwamnatinsa amma ba sa yi

Sauran sun hada da Aminu Kano Way – Kofar Ruwa, Festing – Bompai Road, France Road, Igbo Road, Gwammaja – Wapa Road, Kurna Babban Layi, Madaki Street Yolawa

Bugu da kari akwai aikin hanyoyin, Sabon Titi Mandawari, Kwanar Dala – Gidan Malam Aminu Junction, Lafiya Road, Bello Terrace, Alu Avenue da Iyaka Road.

Daga karshe ya jaddada kudirin gwamnatin Kano na samar da ababen more rayuwa don kyautata rayuwar al’ummar jihar.

Majalisar Wakilai Za Ta Dawo Zama A Ranar 20 Ga Watan Satumba A Zauren Wucin Gadi

A wani labarin, mun ji cewa majalisar wakilai ta kasa za ta dawo zama a ranar 20 ga watan Satumba a zaure na wucin gadi.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga Yahaya Danzaria, magatakardar majalisa a ranar Lahadi, 18 ga watan Satumba a Abuja, jaridar Premium Times ta rahoto.

Mista Danzaria ya ce sakamakon gyare-gyaren da ke gudana a tsohon zauren majalisar, ana sanya ran Mmbobin za su dawo zama a sabon zauren da aka tanada da kujerar zaman mutum 118 kacal.

Kara karanta wannan

'Yan Ta'addan Boko Haram Kasurguman 'Yan Damfara ne, Shugaba Buhari

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel