Bidiyo: Ɗan dambe ya lakaɗi matashin da ya zungure shi a Twitter kuma ya bi shi har gida su goge raini

Bidiyo: Ɗan dambe ya lakaɗi matashin da ya zungure shi a Twitter kuma ya bi shi har gida su goge raini

  • 'Dan dambe ya lakadawa matashi mugun duka bayan da ya tsokane shi kuma ya bi shi har wurin motsa jiki domin su goge raini
  • Matashin mai rabon shan duka, ya kashe har £110 kuma yayi tafiyar mil 200 a jirgin kasa tun daga birnin London domin tarar da 'dan damben
  • Ya kuwa yi sa'a, yana wallafa hotonsa cewa ya isowa wurin, 'dan damben ya garzayo inda ya lakada masa mugun duka

Kwararren 'dan damben Turai, Sunny Edwards ya lakadawa wani wanda ya tsokane shi a Twitter mugun duka bayan ya tashi tun daga London zuwa wurin motsa jikinsa dake Sheffield domin su karasa rikicin da suka fara.

Fab Tanga mai tsautsayin shan duka, ya biya har £110 inda yayi tafiyar mil 200 a jirgin kasa domin damben bayan kwanaki da suka samu sabani a kafar sada zumuntar zamanin.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan fashi da makami sun dura wani coci, sun yiwa fasto da mabiyansa tas

Edward
Bidiyo: Ɗan dambe ya lakaɗi matashin da ya zungure shi a Twitter kuma ya bi shi har gida su goge raini. Hoto daga Michael Benson
Asali: Twitter
Rikicin ya fara ne bayan Tanga ya wallafa a ranar Juma'a, 22 ga watan Yuli cewa: "Na yi alkawari, Sunny Edwards, nayi rantsuwa da rayuwata idan har baka ansa ni ba, safiyar gobe za ka ganni a gaban wurin motsa jikin ka tsakanin 11 zuwa 12. Idan ka bari na kashe kudin da zan ci abinci kuma baka bayyana ba, zan dinga yawo a Sheffield inda bayyana cewa kai rago ne."
Daga baya ya kara da cewa: "A karamin sanin da nayi wa Sunny Edwards, fada kawai nake so in yi da shi. Ta yuwu a yau ba za mu yi bacci ba, ta yuwu Adrenalin din mu ya haskaka dukkan Ingila. Sadauki ne, zai zo, zamu fada a matsayin sadaukai."

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A ranar fadan, Tanga ya ji jiki bayan dakiku kadan da arangama da Edwards bayan lallasa shi da yayi.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Mu muka tallata Buhari, dole mu fito mu fadi gaskiya, Naburaska ya cashe gwamnati

Yayin da Tanga ya isa Yorkshire, ya wallafa hoton shi yayin da yake farfajiyar filin motsa jiki na Edward dake Steel City.

Wannan sakon ya zaburar da shahararren 'dan dambe inda ya garzayo zuwa wurin motsa jikin tare da 'ya'yansa biyu a motarsa.

A bidiyon da ya nada yana kan hanyarsa ta zuwa, ya kuma wallafa a Twitter, Edwards yace: "Ina kan hanyata ta zuwa yanzu. Kada ka je ko ina karamin kwaro."

An nadi fadan kai tsaye inda aka ga yadda Edward ya lallasa Tanga tamkar an masa wahayi.

Hotuna: Ango ya zabi doki matsayin babban abokinsa a aurensa, har amarci ya tafi da shi

A wani labari na daban, wani masoyin doki ya yanke hukuncin amfani da ingarman dokin da yafi kauna a matsayin babban abokinsa a ranar aurensa kuma har ya kai ga tafiya da shi cin amarci.

Paul Boyles mai shekaru 47 ya shirya yadda dokinsa ya taya shi karbar aure a ranar aurensa sa masoyiyarsa Kay mai shekaru 48.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya yi alkawarin yiwa jama'arsa wani abin da Buhari ya gagara yiwa 'yan Najeriya

Asali: Legit.ng

Online view pixel