Bidiyon mahaukaci ya shiga har coci ya rankwashi fasto, ya kwace bibul ya arce

Bidiyon mahaukaci ya shiga har coci ya rankwashi fasto, ya kwace bibul ya arce

  • A wani lamari da yayi kama da zaman bauta, wani mahaukaci ya bayyana tare da tunkarar babban faston ana tsaka da bauta
  • A bidiyon dake ta yawo a kafafen sada zumunta, mahaukacin ya karasa har kan mumbari inda ya rankwashi babban faston a tsakar kai
  • Yayin da limamin da mataimakinsa suka tsaya cike da mamaki, mahaukacin ya kalubalanci wani mai bauta tare da yin awon gaba da bibul

Wani bidiyo dake ta yawo a kafafen sada zumuntar zamani inda wani mahaukaci ya kutsa coci ya janyo cece-kuce.

Wani mutum mai suna Endurance Keyamo wanda ya sha mamaki ne ya wallafa gajeren bidiyon a shafinsa na Facebook a ranar Asabar, 9 ga watan Yulin 2022.

Mahaukaci
Bidiyon mahaukaci ya shiga har coci ya rankwashi fasto, ya kwace bibul ya arce. Hoto daga Endurance Keyamo
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Tantancewa nake yi, har yanzu ban ga nagartaccen namijin da ya dace da ni ba, Jarumar fim mai shekaru 52

Bidiyon mai tsayin dakika 18 ya fara ne da wani mahaukaci mara riga wanda ya hau kan mumbarin coci har zuwa gaban faston cocin.

Ba tare da bata lokaci, ya rankwashi fasto a kai kuma yayi awon gaba da bibul.

Faston da mataimakinsa sun tsaya suna kallon mahaukacin cike da mamaki kuma ba su kalubalance shi ba.

Legit.ng bata iya tantance ingancin bidiyon ba ko kuma lokacin da abun ya faru a lokacin rubuta wannan rahoton.

Latsa nan a kalli bidiyon.

Jama'a sun yi martani

Awudese Ni Perfect yace: "Limaman cocin katolika suna da saiti da natsuwa. Idan da limamin Pentecostal ne, da wannan mahaukacin yaji jiki."
Ekpo Yemi Osinbajo Johnson yace: "Ina ganin mutane na yi wa wannan abu kallo na daban. Mahaukaci zai iya dukan Yesu ko Paul a lokacinsu? Zai ji tsoro ne ko zai nemi gafara? Cocin yanzu ba ita bace Yesu ya kaddamar."

Kara karanta wannan

Bidiyo: Yadda me kula da jakunkuna matafiya ya sace jirgin sama, yayi shawagi a sama, ya tafka hatsari

Idan da mai bukata, a neme ni: Bidiyon dirarriyar BaAmurkiya da tace 'dan Najeriya take son aure

A wani labari na daban, wata budurwa 'yar kasar Amurka ta bayyana bukatarta fili ta son aure namiji 'dan Najeriya. Budurwar da ke bukatar mijin, an ganta a wani bidiyo da ma'abocin amfani da Facebook, Bala Baba Dihis ya wallafa.

Kamar yadda tsokacinsa ya bayyana, budurwar ta bayyana mazaunanta a karshen bidiyon domin jan hankalin mazan.

Da murmushi a fuskarta, budurwar tace tana neman namiji 'dan Najeriya da ke son komawa Amurka kuma su karashe rayuwarsu tare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng