Yanzu-Yanzu: Shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa ya rigamu gidan gaskiya

Yanzu-Yanzu: Shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa ya rigamu gidan gaskiya

  • A yau ne muka samu labarin rasuwar shugaban hadaddiyar daular larabawa Sheilh Khalifa Bn Zayed
  • Rahotanni sun ce, marigayin ya rasu ne bayan fama da doguwar rashin lafiya da ja shi shekaru yana jinya
  • Hakazalika, rahoton ya bayyana yadda shugaban ya shafe shekaru ba a ganinsa a bainar jama'a saboda rashin lafiya

Dubai, UAE - Labari da dumi da muke samu na cewa, shugaban kasar Hadaddiyar Daular Larabawa Sheikh Khalifa bin Zayed Al Nahyan ya rasu yana da shekaru 73, Khaleej Times ta ruwaito.

Wata sanarwar da kamfanin dillacin labarai ta WAM ta yada a Twitter ta ce:

"Ma'aikatar Harkokin Shugaban Kasa ta sanar da cewa za a yi zaman makoki na kwanaki 40 a hukumance tare da sauke tutoci da kuma rufe ma'aikatu da hukumomin gwamnati a matakin tarayya da na kananan hukumomi da kuma kamfanoni masu zaman kansu."

Kara karanta wannan

Sokoto: Tambuwal ya umarci a yi bincike kan kashe dalibar kwalejin da ta zagi Annabi

Allah ya yiwa shugaban UAE ya rasu
Yanzu-Yanzu: Shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa ya rigamu gidan gaskiya | Hoto: timesofisrael.com
Asali: UGC

Sheikh Khalifa, wanda yasha fama da rashin lafiya tsawon shekaru da dama, ya dade da daina shiga harkokin yau da kullum, tare da dan uwansa, Yarima mai jiran gado na Abu Dhabi Mohammed bin Zayed, wanda ake ganin shi ne ke tafiyar da mulki.

Kawo yanzu dai babu sanarwar magajinsa .

Sheikh Khalifa, wanda ba kasafai ake ganinsa a hotuna da wuraren taron jama'a tsawon shekaru, ya gaji mahaifinsa ne kuma wanda ya kafa Hadaddiyar Daular Larabawa, Sheikh Zayed a shekara ta 2004.

Ya yi fama da bugun zuciya shekaru goma bayan zama shugaba, wanda ya sa ba a ganinsa a bainar jama'a tun daga lokacin.

Hasumiya mafi tsayi a duniya a Dubai ta Hadaddiyar Daular Larabawa da ake kira Burj Khalifa tana daukar sunan marigayin ne, kamar yadda Al-Jazeera ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Sokoto: Bishop Kukah ya yi martani kan kashe dalibar da ta yi batanci ga Annabi

Gwarzon Dimokradiyya: Za a karrama shugaba Buhari da babbar lambar yabo

A wani labarin, nan ba da jimawa ba za a karrama shugaban kasa Muhammadu Buhari da lambar yabo ta gwarzon dimokuradiyya, wanda majalisar ba da shawara ta jam’iyyu (IPAC) za ta ba shi.

Jaridar PM News ta ruwaito cewa, Engr. Yusuf Yabagi, shugaban jam'iyyar ADP kuma kodinetan IPAC ne ya sanar da hakan a ranar Talata 26 ga watan Afrilu yayin wata liyafar buda baki da Buhari a Abuja.

Yabagi ya ce za a karrama Buhari ne saboda sanya hannu a kan dokar zabe mai dumbun tarihi domin tana wakiltar sauyi da zai tabbatar da zaman lafiya da karbuwa da zabuka a kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel