Saudi Arabia ta ƙaddamarwa mutum 81 hukuncin kisa a rana ɗaya

Saudi Arabia ta ƙaddamarwa mutum 81 hukuncin kisa a rana ɗaya

  • Masarautar Saudiyya ta sanar da kaddamar wa mutum 81 hukuncin kisa a kasar bayan alkalai 13 sun yanke musu hukunci
  • Kamar yadda masarautar ta sanar, laifukansu sun hada da ta'addanci, kisan kai, biyayya ga kungiyoyin ISIS da Al-Qaeda da sauransu
  • Wannan ne mafi yawan mutane da aka kaddamarwa da hukuncin kisa a tarihin kasar a rana daya kan miyagun laifuka

Masarautar Saudi Arabia a ranar Asabar ta sanar da cewa ta kaddamar wa mutum tamanin da daya hukuncin kisa bayan an yanke musu hukunci.

Sanarwar ranar Asabar din ita ce sanarwar kaddamar da hukuncin kisan kai mafi yawa a tarihin masarautar, fiye da sittin da bakwai da aka yi a shekarar 2021 da 27 na shekarar 2020, Al-Jazeera ta ruwaito.

Kara karanta wannan

'Dan Majalisar Najeriya: Babu Korona a Najeriya, Mu Daina Amfani Da Takunkumin Fuska

Kafin ranar Asabar, a tarihin kasar tun daga 1980, mafi yawan hukuncin kisa da aka kaddamar shi ne a 2016 inda aka kashe mutum 47.

Sai dai kuma, an zarce wannan yawan na 1980 yayin da aka halaka wasu tsageru 63 bayan yanke musu hukunci.

Saudi Arabia ta ƙaddamarwa mutum 81 hukuncin kisa a rana ɗaya
Saudi Arabia ta ƙaddamarwa mutum 81 hukuncin kisa a rana ɗaya. Hoto daga thecable.ng
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda cibiyar yada labarai ta Saudi ta sanar, an yanke wa mutum tamanin da biyar din hukunci ne kan laifukan ta'addanci da wasu manyan laifuka.

SPA ta ce wadanda aka yi wa wannan hukuncin sun hada da mambobin al-Qaeda, ISIS da kuma masu goyon bayan tsagerun Houthi na Yemen.

Daga cikin mutanen tamanin da daya, 73 'yan kasar Saudi ne yayin da 7 'yan kasar Yemen ne sai mutum 1 dan kasar Syria, TheCable ta ruwaito.

"Wadannan mutanen an yanke musu hukunci ne sakamakon laifukan kisan mutane, maza, mata da kananan yara," SPA tace yayin da take debo bayanin ma'aikatar cikin gida.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Yan bindiga sun buɗe wa mutane wuta a Kaduna, rayuka sun salwanta

"Laifukan da wadannan suka aikata sun hada da biyayya ga kungiyoyin ta'addanci na duniya da suka hada da ISIS, Al-Qaeda da kuma Houthis, sun yi kokarin kai farmaki ga mazauna masarautar da kuma garzayawa yankunan rikici domin hadewa da kungiyoyin ta'addanci."

Kamfanin Labaran ya ce an kama su da laifin yunkurin kai wa jami'an gwamnati farmaki da wasu fannonin tattalin arziki, kashe jami'an tsaro da kuma lalata gawawwakinsu da kuma saka nakiya a motocin 'yan sanda.

Bayan kisa, an kama su da laifin garkuwa da mutane, azabtarwa, fyade da shigar da makamai da bama-bamai cikin kasa.

Kamar yadda SPA tace, alkalai 13 ne suka tuhumi masu laifin kuma an bi matakin shari'a har uku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel