Dan Majalisar Najeriya: Babu Korona a Najeriya, Mu Daina Amfani Da Takunkumin Fuska

Dan Majalisar Najeriya: Babu Korona a Najeriya, Mu Daina Amfani Da Takunkumin Fuska

  • Wani dan majalisa mai wakiltar mazabar Alimosho da ke Legas, Olufemi Adebanjo, ya ce yanzu haka cutar COVID-19 ta kare a kasar nan
  • Ya yi wannan maganar ne a ranar Alhamis inda yace ya kamata a daina sanya takunkumin fuska duba da yadda mutane suka daina kamuwa da cutar
  • A cewarsa, kusan watanni biyu kenan da ba a sake samun wani mai cutar ba a Najeriya, duk da dai maganar sa ta ci karo da kidayar NCDC

Abuja - Olufemi Adebanjo, wani dan majalisar wakilai ya ce mutane ba sa kamuwa da cutar COVID-19 a kasar nan, hakan ya na nuna ta kare kenan, The Cable ta ruwaito.

Adebanjo, dan majalisa mai wakiltar mazabar Alimosho da ke Jihar Legas a majalisar wakilai ta tarayya ya yi wannan maganar a cikin majalisar ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

2023: Kamata Ya Yi PDP Ta Nemi Gafara Daga Ƴan Najeriya, Ba Kuri'unsu Ba, Lawan

Dan Majalisar Najeriya: Babu Korona a Najeriya, Mu Daina Amfani Da Takunkumin Fuska
Dan Majalisar Najeriya: Korona Ta Kare a Najeriya, Mu Daina Amfani Da Takunkumin Fuska. Hoto: The Cable
Asali: Twitter

A cewarsa, daga Najeriya har kasar waje ba a samun masu kamuwa da cutar COVID-19 tsawon watanni 2 da suka gabata, hakan yasa ya bukaci a daina sanya takunkumin fuska a majalisar.

Maganarsa ta ci karo da alkalluman NCDC

Sai dai maganar Adebanjo ta ci karo da kidayar cibiyar dakatar da yaduwar cutuka ta Najeriya, NCDC wacce kusan kullum sai ta bayyana an kamu da cutar COVID-19.

Misali, a ranar Alhamis NCDC ta bayyana yadda mutane 84 suka kamu da cutar, jajibarin ranar da ya bukaci a dakatar da wannan dokar.

Yayin da yake korafin babu takunkumi a fuskarsa

A cewarsa yayin da bai sanya takunkumin fuska ba:

“Ina son sanar da majalisar tarayya, musamman bangaren wakilai dangane da sanya takunkumin fuska da muke yi kullum idan zamu zo majalisa.

Kara karanta wannan

Yin arziki 'yan Crypto zai tabbata: Amurka ta juyo kan 'yan Crypto, za su ga canji nan kusa

“Kusan watanni 2 da suka gabata, bamu sake jin batun COVID-19 ba a Najeriya da kasar waje. Sanya takunkumin fuska yana da wahala sosai kuma ya kamata a sassauta mana sanya shi. Idan ka duba, yanzu haka babu wasu mutanen da ke sanye da takunkumi.
“Yana matukar wahalar da mu wurin numfashi. Babu COVID-19 a Najeriya, kuma babu cutar a kasar waje.”

Mataimakin kakakin majalisar ya ce ba su da hurumin dage dokar

Yayin mayar masa da martani bisa ruwayar The Cable, mataimakin kakakin majalisar, Idris Wase ya ce ba majalisar tarayya bace ta ke da alhakin dakatar da dokar kare ka daga COVID-19.

Kamar yadda ya ce:

“A matsayin mu na ‘yan majalisa, bai dace mu dinga cece-kuce akan dokoki ba, ko kuma kundin tsarin mulkin Najeriya, NCDC ce ta ke da alhakin sanya doka ko ta cire.”

Ya ce duk da dai kakakin su ba ya kan aiki, zai shawarci kowa akan ci gaba da kiyaye dokokin da aka kafa a ciki da wajen kasa.

A cewarsa lokacin da dan majalisar yake maganar ya kula babu takunkumin fuska a tare da shi, amma ya ji dadin yadda ya sanya daga baya kuma an saurari nashi korafin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Online view pixel