Mutuwar auren Bill Gates ta sa ya sullubo daga na 4 a jerin manyan Attajiran Duniya

Mutuwar auren Bill Gates ta sa ya sullubo daga na 4 a jerin manyan Attajiran Duniya

  • Dukiyar Bill Gates ta yi kasa a sanadiyyar sakin matarsa, Melinda French Gates
  • Melinda French Gates ta samu makudan kudi bayan ta rabu da babban Attajirin
  • Mark Zuckerberg ya kerewa Bill Gates a jerin masu kudin Duniya a halin yanzu

USA - Mujallar Forbes ta ce Melinda French Gates ta mallaki kimanin fam Dala $5.6 a halin yanzu, hakan na zuwa ne bayan ta rabu da mai gidanta, Bill Gates.

Rahoton yace kudin da Bill Gates ya ba tsohuwar mai dakinsa a sakamakon mutuwar aurensu, ya sa ya sauka daga mutum na hudu a jeringiyar Attajiran Duniya.

Wanene ya sha gaban Bill Gates a 2021?

Forbes ta ce abin da Bill Gates ya mallaka a halin yanzu bai zarce fam Dala biliyan 129.6 ba. Hakan ya sa mai Facebook, Mark Zuckerberg ya sha gaban shi kadan.

Shugaban kamfanin Facebook, Zuckerberg mai shekara 37 ne na hudu a Duniya, yayin da Bill Gates ke rike da matsayin mutum na biyar da ya fi kowa kudi.

Nawa Melinda French-Gates ta samu?

A al’ada, idan ma’aurata suka rabu, mata za ta samu kaso a dukiyar mijin. A shekarar nan ne auren Gates ya mutu bayan sun shafe shekaru kusan 30 suna tare.

Bloomberg ta ce kamfanin Gates na Cascade Investment LLC ya tura wa Melinda French Gates kusan dala biliyan $2.4 a asusunta a ranar Alhamis da ta wuce.

Mutuwar auren Bill Gates
Bill da Melinda Gates Hoto: www.bbc.com
Asali: UGC

Hakan na zuwa ne bayan Gates ya ba tsohuwar mai dakinsa Dala biliyan $3.2 jim kadan bayan aurensu ya mutu a watan Mayu, hakan ya sa dukiyarta ta karu.

Melinda French-Gates ta tashi da hannun jari miliyan 3.3 a kamfanin AutoNation, kudin da ya kai Dala miliyan 400, yanzu ta mallaki 8% na jarin kamfanin motocin.

Har ila yau, French ta samu hannun jari miliyan 2.8 a kamfanin Cascade masu kirkirar kayan gona, ta kuma samu Dala biliyan 1 daga kamfanin jirgin Kanada.

Har zuwa yanzu ba za a iya cewa ga adadin dukiyar da uwar ‘ya ‘yan Bill Gates din za ta tashi da shi ba.

Mutuwar auren bai raba Gates ba

Bill da Melinda sun hadu ne tun a 1987 kuma sun yi aure a shekarar 1994. Shekaru fiye da 20 da su ka wuce, suka kafa gidauniyarsu, a bana igiyar aurensu ya tsinke.

Rahoton kotu ya nuna cewa babu wanda zai canja sunansa a cikinsu duk da sun rabu. Wadannan mutane za su cigaba da aiki tare a gudauniyar su ta Bill & Melinda.

Asali: Legit.ng

Online view pixel