Solomon Dalung ya nemi a yafe masa na yi wa APC kamfe, ya bi Kwankwaso zuwa TMN

Solomon Dalung ya nemi a yafe masa na yi wa APC kamfe, ya bi Kwankwaso zuwa TMN

  • Tsohon ministan wasanni na kasa, Solomon Dalung ya yi tir da gwamnatin Muhammadu Buhari
  • Solomon Dalung ya yarda Gwamnatinsu ta APC ta gaza, ya na cikin wadanda suka shiga tafiyar TMN
  • A cewar jagoran na APC, jam’iyyarsu ta gaza cika duk alkawuran da tayi, ya kamata a ba jama’a hakuri

Abuja - Premium Times ta kawo rahoto a ranar Talata, inda aka ji tsohon Ministan wasanni yana ganin kwalliya ba ta biya kudin sabulu a mulkin APC ba.

Duk da cewa da su aka fara tafiyar APC, da yake magana wajen kaddamar da tafiyar TNM, Solomon Dalung ya koka cewa gwamnati mai-ci ta gaza.

A jawabinsa, Dalung ya ce duk wasu ma’aunan da za a dauka sun nuna abubuwa sun tabarbare.

Kara karanta wannan

Duk da sun kafa TMN, Kwankwaso ya na nan daram-dam-dam a jam’iyyar PDP

“Yadda nake tsaye a nan, mutane su na iya tuna fuska ta wajen jawo jama’a tsakanin 2009 da 2015. Da farko mun fara da yi wa gwamnatin Jonathan adawa.”
“Ni ne wanda ya fara yi wa Jonathan adawa tun da aka saba kundin tsarin mulkin Najeriya, aka rantsar da shi a matsayin shugaban kasa na rikon kwarya.”
“Jam’iyyar APC ta same ni ina hamayya. Amma yau, ya kamata mu fara da ba mutanen Najeriya hakuri, dole ne (gwamnatin APC) mu nemi afuwa da gaske.”
- Solomon Dalung
Bikin TMN
Taron kaddamar da TMN Hoto: Saifullahi Hassan
Asali: Facebook

Ba haka mu ka yi a 2015 ba

“Domin ba mu yi masu alkawari ‘Yan Najeriya za su saye shinkafa a kan N35, 000 ba, a maimakon N7, 000 da mu ka samu farashin buhu da muka hau mulki.”

Kara karanta wannan

Abubuwa 10 da Kwankwaso ya fada wajen kaddamar da sabuwar tafiyar siyasarsu

Jaridar ta ce Dalung ya ba mutanen kasar hakuri kan rawar da ya taka wajen karkato da ra’ayinsu, ya ce bayan shekaru shida, ba a cika alkawuran da aka yi ba.

Ubangiji zai tsaida da ni - Dalung

‘Dan siyasar ya ce a matsayinsa na kirista mai tunani, dole ya ba mutane hakuri domin za a tambaye shi a ranar hisabi, inda kaunar APC ba za tayi masa aiki ba.

“A matsayina na kirista mai tunani, dole in nemi afuwa a Najeriya domin bayan wannan Duniyar, za mu je gaban Ubangiji a ranar hisabi.”
“Daga cikin tambayar da za ayi shi ne, 'Solomon Dalung ka tattaro kan ‘Yan Najeriya, da ake kashe mutane, ana yi masu fyade, me ka fada.'”

- Solomon Dalung

An yanka cibiyar TMN

Ku na da labari cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwanso sun kafa sabuwar kungiyar siyasa ta TMN domin karbe mulki a hannun APC

Kara karanta wannan

Tuna baya: Abin da APC ta fada sa’ilin da ASUU ta yi dogon yajin-aiki a mulkin Jonathan

Wadanda ke tare da Sanata Kwankwaso sun hada tsohon ministan wasannin Najeriya, Solomon Dalung, Sanata Suleiman Hunkuyi, da Injiniya Buba Galadima.

Asali: Legit.ng

Online view pixel