Tsoho mai shekaru 94 ya koma gida a talauce bayan yin shekaru 42 yana neman arziki

Tsoho mai shekaru 94 ya koma gida a talauce bayan yin shekaru 42 yana neman arziki

  • Hiltan Kalugho tsoho ne mai shekaru 94 a duniya da ya kwashe shekaru 42 da barin gida domin neman arziki
  • Sai dai bayan gwada sana'o'i daban-daban, tsohon bai samu komai ba na arzikin duniya don haka ya tattara ya koma gida
  • A cewar tsohon, ya tarar da matarsa da 'ya'yansa biyu sun rasu kuma ya yi takaicin rashin saduwarsu bayan tsawon shekaru

Wani mutum mai shekaru 94, dan kasar Kenya, ya koma ga iyalinshi a kauyen Majengo, Mwatate da ke alkaryar Taita-Taveta bayan daukar shekaru 42 da barin gida.

Hiltan Kalugho ya bada labarin yadda ya bar matarsa da yara bakwai a gida zuwa Tanzania a shekarar 1980 don neman arziki a kasar dake makwabtaka da su.

Tsoho mai shekaru 94 ya koma gida a talauce bayan yin shekaru 42 a Turai yana neman arziki
Tsoho mai shekaru 94 ya koma gida a talauce bayan yin shekaru 42 a Turai yana neman arziki. Hoto daga Nation Africa
Asali: UGC
"Na bar gida don neman abun rayuwa, saboda yadda naso wa yara na rayuwa mai kyau a gaba. Sai dai, na kasa dawowa gida saboda ban samu kudin da nake sa ran daukar ragamar iyali na ba," ya bayyana wa Sunday Nation.

Kara karanta wannan

Muna hanyar zuwa Kebbi daurin aure aka ce yan bindiga sun tare hanya, Shehu Sani

Ban samu arzikin da nake nema ba

Kamar yadda tsohon ya bayyana, yayi rayuwar shi a iyakar birnin Mororoni, inda yayi aiki da farko a matsayin mai hako ma'adanai, sai dai bai kai mishi yadda yake fata ba, hakan ya tilasta shi gwada kiwon dabbobi.

"Ba na samun wata riba. Abunda nake samu, kawai ya na isar mu rayuwa ne," a cewar Kalugho.

Yadda ya koma gida

A wannan lokacin, Kalugho ya ce, ya ki sake wani auren, yayin da ya fara haramar dawowa gida. Inda wani fasto dan kasar Kenya, wanda ya ziyarci yankin ya bada labarin Kalugho a kafafan sada zumuntar zamani, hakan ya taimaka mishi wajen sake hada shi da iyalin shi.

Yaron Kalugho, Mnjala Mwaluma, ya ce bayan daukar tsawon shekaru suna neman mahaifin nasu, wani fasto ya kira shi, inda ya shaida masa cewa ya hadu da shi a kasar Tanzania.

Kara karanta wannan

Kaduna: Ina shirin aurar da 2 daga cikin 'ya'yana mata da aka sace, Basarake

"Ban dade da samun kira daga fasto ba, ga mamaki na yake shaida mini cewa, an gano mahaifi na a Tanzania. Ya tafi da ni zuwa Mombasa, inda muka hadu dashi," a cewar Mwaluma.

Kalugho ya dawo gida a satin da ya gabata, ya tarar matarsa da yaran shi maza guda biyu sun rasu tun shekarar 2007.

"Raina bai min dadi ba da ban samu wasu daga cikin iyali na su shaida wannan sada zumuncin ba. Na yi burin ganin mata ta da duka yara na." A cewarsa.

Bayan ƙodarta ta yi ɓatan dabo daga zuwa Saudiyya, za a biya ta N31.8M diyya

A wani labari na daban, Judith Nakintu, wata mata 'yar kasar Uganda wacce aka cire mata koda a kasar Saudi Arabia ba tare da izninta ba, za a biya ta miliyoyi.

Kamfanin kwadago na Nile Treasure da ya dauka Judith zuwa Jeddah ya ce sun yarda cewa tsohon ubangidanta, Saad Dhafer ya ce wani mugun hatsari ya ritsa da ita.

Kara karanta wannan

Matashi a Kano,Tijjani, ya sha fiya-fiya bayan samun labarin budurwarsa zata auri maikudi

Asali: Legit.ng

Online view pixel