Ministar mata tayi kira ga maza da su dinga dukan matansu masu taurin kai, hakan ya janyo cece-kuce

Ministar mata tayi kira ga maza da su dinga dukan matansu masu taurin kai, hakan ya janyo cece-kuce

  • Minsitar mata , iyalai da habaka yankuna a kasar Malaysia ta shawarci maza da su dinga dukan matansu masu taurin kai
  • A cewar ministan, kada mata su kuskura su tattauna da mazansu kan har sai sun gansu cikin nishadi bayan sun ci abinci tare da hutawa
  • Wannan batun ya tada kayar baya inda kungiyoyin daidaiton jinsi suka yi caa kan ministar a zarginta da suke wurin assasa cin zarafin mata

Wata minista mace a Malaysia ta janyo cece-kuce bayan ta shawarci maza da su dinga dukan matansu masu taurin kai amma a tausashe domin ladabtar da su daga miyagun dabi'u.

Sitit Zallah Mohd Yusoff, mataimakiyar ministan harkokin mata, iyalai da habaka yankuna, an zarge ta da assasa cin zarafi ta yadda ta shawarci maza da su zama masu kaushi ga matansu, Daily Mail ta ruwaito.

Kara karanta wannan

An maka dalibi mai shekaru 21 a kotu kan tura wa mijin budurwarsa hotunan tsiraicinta

Ministar mata tayi kira ga maza da su dinga dukan matansu masu taurin kai, hakan ya janyo cece-kuce
Ministar mata tayi kira ga maza da su dinga dukan matansu masu taurin kai, hakan ya janyo cece-kuce. Hoto daga dailymail.co.uk
Asali: UGC

A bidiyo mai tsayin mintina biyu da ta wallafa a Instagram kuma ta yi masa take da "Mother's Tips", mataimakiyar ministan da farko ta shawarci maza da su ladabtar da matansu masu taurin kai ta hanyar zaunar da su suyi musu magana. Amma idan ba su canza ba daga dabi'unsu, sai su kaurace musu a wurin kwanciya na kwanaki uku.

Idan har a lokacin macen bata sauya hali ba, toh mijin ya zaneta domin nuna tsantsaini da suka yadda yake son ta canza, Siti Zailah tace a bidiyon, Daily Mail ta rahoto.

Siti Zailah Mohd Yusoff mataimakiyar ministar harkokin mata, iyalai da habaka zamantakewa, wacce mamba ce a jam'iyyar musulunci ta Malaysia, ta kara da kira ga mata da su tattauna da mazansu ne a lokutan da mazan suka basu dama domin shawo kansu.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: An sake yi wa matafiya 'yan Kano da Nassarawa kisar gilla a hanyar Jos

"Ku yi magana da mazan ku na aure a tausashe, bayan ya kammala cin abinci, ya yi sallah kuma ya na hutawa. Idan kuma za ku musu magana, ku nemi izini kafin ku fada," tace.

Kungiyar gamayyar kare hakkin mata tare da tabbatar da daidaiton jinsi, ta zargi Siti Zailah da assasa cin zarafi tare da bukatar ta yi murabus daga matsayin ta.

"Dole ne mataimakiyar ministan ta yi murabus saboda yadda ta assasa cin zarafi wanda babban laifi ne a Malaysia, tare da bayyana shawara da dabi'u da suka ci karo da daidaituwar jinsi," takardar hadin guiwar yace.

Kungiyar ta ce tsakanin 2020 zuwa 2021, an samu rahotannin da aka kai wa 'yan sanda 9,015 kan cin zarafin mata a cikin gida, kuma wannan ta yuwu ya fi hakan saboda ba a hada da korafin da mata suka kai wa kungiyoyin tallafi ba.

Sun kara da cewa: "A matsayin ta na minista wacce ake sa ran za ta assasa daidaiton jinsi da kare hakkin mata, wannan abun ashsha ne ta yadda ta ke kokarin danne hakkin mata da kuma bada shawarar cin zarafinsu."

Kara karanta wannan

Kaduna: Kotun Shari'a Ta Tura Kishiyoyi 2 Zuwa Gidan Yari Saboda Faɗa Kan Mijinsu, Mijin Ya Ce Akwai Yiwuwar Ya Sake Su Duka

An maka dalibi mai shekaru 21 a kotu kan tura wa mijin budurwarsa hotunan tsiraicinta

A wani labari na daban, ana tuhumar wani dalibi dan kasar Kenya mai shekaru 21 da zargi kan cin zarafin mijin wata wacce ake zargi da zama masoyiyar sa, bayan ya tura mishi hoton tsiraici na sirrin matar sa.

Wanda ake zargin, Steven Wanjohi Kamande, ya bayyana gaban babban alkalin majistare Wendy Kagendo na kotun shari'a ta Milimani a ranar Litinin, 14 ga watan Fabrairu, shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

Ya musanta laifuka ukun da ake zargin sa da su, na tura mishi bayanin kanzon kurege, barazana ga rayuwar shi da gangancin yada ababen da basu dace ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel