Allah ya yiwa babban Malamin addini, Sheikh Saleh Al-Luhaidan, rasuwa
- Daya daga cikin manyan Malaman addinin Musulunci a duniya ya rigamu gidan gaskiya
- Manyan Malamai, daliban ilimi, yan uwa da abokan arziki sun yi alhini da addu'an Allah ya jikan Malamin.
- Sheikh Al-Luhaydan mamba ne na majalisar malamai a kasar Saudiyya gabanin rasuwarsa
RIYADH — Babban Malamin addinin Musulunci, dan kasar Saudiyya, Sheikh Saleh Al-Luhaidan, ya rigamu gidan gaskiya bayan doguwar jinyar rashin lafiya.
Iyalan Shehin Malamin suka sanar da mutuwarsa a shafin Tuwita, inda suka bayyana cewa ya yi fama a rashin lafiya sosai.
Sheikh Saleh Al-Luhaidan ya rasu yana mai shekaru 90 a duniya.
An yi masa Sallar Jana'iza da rana a Riyadh, babbar birnin kasar Saudiyya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wanene Sheikh Saleh Al-Luhaidan?
An haifi Sheikh Al-Luhaidan a garin Bukayriyah dage yankin Al-Qassim a shekarar 1931.
Ya rike mukamai da dama, wanda ya hada da mamban Majalisin manyan Malamai, mamban kungiyar Musulmai ta duniya kuma tsohon Shugaban majalisar koli ta Shariah
A shekarar 1979, shine wanda yayi khudubar aikin Hajji.
Manyan Malamai, daliban ilimi, yan uwa da abokan arziki sun yi alhini da addu'an Allah ya jikan Malamin.
Asali: Legit.ng