An yanke wa tsohon shugaban gidan yari ɗaurin shekaru 5 saboda yi wa furusuna sata

An yanke wa tsohon shugaban gidan yari ɗaurin shekaru 5 saboda yi wa furusuna sata

  • Wata kotu a kasar Rwanda ta yanke wa tsohon shugaban gidan yari, Innocent Kayumba hukuncin daurin shekaru 5 a gidan kaso
  • An yanke wa Kayumba wannan hukuncin ne bayan samunsa da sace wa wani fursuna kudi kimanin £7,000 ($9,300) ta katin ATM
  • Kotun ta gano cewa Kayumba da mataimakinsa sun tilastawa wani fursunan, kwararre a fannin sadarwa yin kutsen ne amma shi kotun ta wanke shi

Rwanda - An yanke wa tsohon shugaban gidan yari hukuncin daurin shekaru biyar saboda yi wa wani fursuna dan kasar Birtaniya sata, LIB ta ruwaito.

Innocent Kayumba da tsohon mataimakinsa Eric Ntakirutimana, sun daukaka kara kan hukuncin da kotun Rwanda ta yanke musu, kamar yadda takardu suka nuna.

An yanke wa tsohon shugaban gidan yari daurin shekaru 5 saboda yi wa furusuna sata
Tsohon shugaban gidan yari ya yi wa fursuna sata, an yanke masa daurin shekaru 5 a gidan yari. Hoto: LIB
Asali: Facebook

Kayumba ya tilastawa wani fursunan yin kutse a katin ATM

Kara karanta wannan

Bidiyon Ƙasaitattun Kayan Alatu Da Matashi Ya Saka a Gidansa Na Kasa, Ciki Har Da AC, Babban TV Da Kujeru

LIB ta ruwaito cewa kafin a yanke masa hukuncin daurin, kotun ta wanke wani kwararren mai ilimin sadarwa wanda ya yi amfani da basirarsa ya kutsa katin cire kudi na wanda aka yi wa satar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kwararren ya bayyana wa kotu cewa tsohon shugaban gidan yarin ne ya tilasta masa yin kutsen. Ya kuma ce jami'an gidan yarin sun bukaci ya 'bude' katin ne bayan sun gano akwai makuden kudi a asusun bankin fursunan.

Dan kasar Birtaniyan da Egypt da ke gidan yarin ya shaida wa kotu cewa an sace masa zunzurutun kudi fiye da £7,000 ($9,300) ta hanyar amfani da katinsa ba tare da saninsa ba.

Kotun ta yanke hukuncin cewa Mr Kayumba da mataimakinsa ne suka hada baki suka yi satan, yayin da shi kuma kwararren mai ilimin sadarwar tilasta masa aka yi, hakan yasa aka wanke shi.

Kara karanta wannan

An yanke wa tsohuwar shugaban kasar Myanmar hukuncin shekaru 4 a gidan yari

Mr Kayumba, tsohon babban jami'in soja ne, an tura shi sashin kula da gidan yari a shekarar 2014. Ya shugabanci gidan yari a yammacin Rwanda kafin a mayar da shi babban birnin kasar.

An kama shi a farkon wannan shekarar.

An sha mamaki bayan gano cewa gardin namiji aka tura gidan yari na mata ba tare da an gane a kotu ba

A wani rahoton, wani lamari mai ban mamaki ya auku a gidan gyaran halin mata da ke Shurugwu a makon da ya gabata, inda aka gano wata fursuna ba mace bace, katon namiji ne kamar yadda LIB ta ruwaito.

Praise Mpofu mai shekaru 22 ya na sanye da suturar mata ne a lokacin da aka kama shi inda ya bayyana kamar karuwa don ya yaudari maza ya yi musu sata.

An kama Mpofu ne bayan ya yi wa wani mutum da ke yankin Gweru sata. An samu rahoto akan yadda mutumin ya caskewa Mpofu kudi don su kwana tare da shi a tunanin sa mace ne, daga nan Mpofu ya yashe shi ya tsere.

Asali: Legit.ng

Online view pixel