An yanke wa tsohuwar shugaban kasar Myanmar hukuncin shekaru 4 a gidan yari

An yanke wa tsohuwar shugaban kasar Myanmar hukuncin shekaru 4 a gidan yari

  • An yanke wa tsohuwar shugaban kasar Myanmar, Aung San Suu Kyi, hukuncin daurin shekaru 4 a gidan yari
  • Hakan ya biyo bayan samun ta da aikata laifukan hure wa mutane kunne da karya dokokin annobar korona ne a kasar
  • Har wa yau, kotun ta gabatar da wasu tuhume-tuhume 11 a kanta har da masu alaka da rashawa amma ta musanta dukkan su

Myanmar - Wata kotu ta musamman ta yanke wa Aung San Suu Kyi, tsohuwar shugaban kasar Myanmar hukuncin daurin shekaru hudu a gidan yari, The Cable ta ruwaito.

An same ta da laifukan hure wa mutane kunne su yi bore da kuma karya dokokin dakile yaduwar annobar korona a kasar.

Suu Kyi ta kasance a tsare tun bayan da sojojin kasar suka hambarar da gwamnatin farar hula a ranar 1 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta bayyana dalilin ta na garkame ofishin lauyan Shekarau

An yanke wa tsohuwar shugaban kasar Myanmar hukuncin shekaru 4 a gidan yari
An yanke wa Aung San Suu Kyi Myanmar hukuncin shekaru 4 a gidan yari. Hoto: The Cable
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Juyin mulkin na zuwa ne shekaru 10 bayan da sojojin suka mika wa farar hula mulki a kasar.

Myanmar ta kasance a karkashin mulkin sojoji har sai da aka fara samun sauye-sauyen demokradiyya a shekarar 2011.

Suu Kyi ta musanta zargin da aka mata

Tsohuwar shugaban tana fuskantar tuhuma guda 11 amma ta musanta aikata dukkan laifukan.

Sauran tuhume-tuhumen sun hada da rashawa, saba dokokin kasa da dokar sadarwa.

Idan an same ta da laifi, za a iya yanke mata hukuncin daurin fiye da shekaru 100 a gidan yari.

A ranar Litinin, kotu ta daure Win Myint, tsohon shugaban kasa kuma aminin Suu Kyi bisa tuhuma iri daya.

A halin yanzu ba a san ko za a tura su gidan yari nan take bane ko kuma za a saurari shari'ar sauran tuhume-tuhumen da ake musu.

Kara karanta wannan

Da duminsa: Hukumar EFCC ta sake Femi Fani-Kayode, bayan tasa keyarsa a kotu

An sha mamaki bayan gano cewa gardin namiji aka tura gidan yari na mata ba tare da an gane a kotu ba

Wani lamari mai ban mamaki ya auku a gidan gyaran halin mata da ke Shurugwu a makon da ya gabata, inda aka gano wata fursuna ba mace bace, katon namiji ne kamar yadda LIB ta ruwaito.

Praise Mpofu mai shekaru 22 ya na sanye da suturar mata ne a lokacin da aka kama shi inda ya bayyana kamar karuwa don ya yaudari maza ya yi musu sata.

An kama Mpofu ne bayan ya yi wa wani mutum da ke yankin Gweru sata. An samu rahoto akan yadda mutumin ya caskewa Mpofu kudi don su kwana tare da shi a tunanin sa mace ne, daga nan Mpofu ya yashe shi ya tsere.

Asali: Legit.ng

Online view pixel