Nan da shekaru 7 duniya za ta tashi, Baturen da ke zama a kangon gini ya magantu

Nan da shekaru 7 duniya za ta tashi, Baturen da ke zama a kangon gini ya magantu

  • Wani bature da ke zama a yasasshen kango a Amurka ya ce ba ya da shirin barin kangon da yake zama ciki ko kuma gyara ginin
  • Mutumin mai shekaru 53, Leslie Southam ya yarda da cewa duniya tana gab da tashi nan ba da dadewa ba
  • A cewarsa nan da shekaru 7 duniya zata zo karshe kuma ya bayyana alamomin da ya gani da suke nuna masa hakan

Yayin da wasu suke kokarin aure wasu kuma su na ta kokarin nemo nasarorin rayuwa ko tara ababen duniya, akwai wadanda ke ganin duniya ta kusa karewa.

Nan da shekaru 7 duniya za ta tashi, Baturen da ke zama a kangon gini ya magantu
Yana jiran tashin dnuniya. Hoto: The Mirror
Asali: UGC

Leslie Southam mai shekaru 53 ya ce nan da shekaru 7 duniya zata zo karshe kuma yanzu hakan zaman jiran lokacin yake yi.

Kara karanta wannan

A cikin shekaru 3, motoci 30 na sata, Wanda ake zargi da fashi da makami

Jaridar The Sun ta ruwaito cewa har yanzu Leslie yana ci gaba da rayuwa cikin wani tsohon kango da ke Brynmefys a Wales da ke cikin Amurka tare da iyayensa da suka tsufa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An siya kangon da suke zama a ciki ne tun shekarar 1980 da doriya amma har yanzu ba a taba gyarawa ba duk da yadda mutane ke ta kwankwasa gine-gine.

Dalilinsa na yarda cewa duniya ta kusa zuwa karshe

A wata hira da Wales Online ta yi da Laslie, ya sanar da cewa ko annobar Coronavirus ma alama ce ta zuwan karshen duniya.

Ya bayyana cewa ko lalacewar gine-gine, tarin bololi da tsatar da saman kwanon jama’a yake yi ma duk alama ce da ke nuna cewa kasa tana son lashe komai.

Ya ce duk alamu ne da ke nuna cewa Jesus ya kusa bayyana. Kamar yadda ya shaida:

Kara karanta wannan

Fannin shari'ar kasar nan ba zai sassauta ba sai ya ga bayan rashawa, CJN Tanko

“Yanayin yadda abubuwa ke tafiya, ba zai wuce shekaru 7 ba, duniya za ta kare.”

Bayan rayuwa cikin daji yana cin ciyawa, yanzu wankan sutturu na alfarma ya ke yi, ana girmama shi a gari

A wani rahoton, wani matashi, Nsanzimana Elie ya kasance a baya ya na zama cikin daji saboda yanayin suffar sa, sannan mutanen kauyen sa har tonon sa su ke yi.

Akwai wadanda su ke kiran sa da biri, ashe daukaka ta na nan biye da shi, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Mahaifiyar Elie ta ce Ubangiji ya amshi addu’ar ta na ba ta shi da ya yi bayan yaran ta biyar duk sun rasu, kuma ba ta kunyar nuna shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel