Da baki bari an haifeni ba: Budurwa ta shigar da Likitar da ta karbi haihuwarta kotu

Da baki bari an haifeni ba: Budurwa ta shigar da Likitar da ta karbi haihuwarta kotu

  • Wata budurwa yar shekara 20, Evie Toombes, ta shigar da Likitar da ta kula da mahaifiyarta lokacin da take dauke da cikinta
  • Evie Toombes, tace da likitar ta baiwa mahaifiyarta shawarar da ya kamata kan maganin Folic Acid, da bata haifeta da nakasa ba
  • Likitar mai suna, Mitchell, ta musanta zargin cewa bata baiwa mahaifiyar budurwar shawarar magungunan da ya kamata ta sha lokacin da take dauka da juna biyu ba

Wata budurwa mai suna Evie Toombes, mai cutar Spina Bifida, ta kai karar Likitarta da kula da mahaifiyarta lokacin da take dauke da cikinta shekaru 20 da suka gabata.

A cewarta, Likitar ta ki baiwa mahaifiyarta shawara ta sha wasu magunguna da ka iya kawar da cutar lokacin da take cikin mahaifa, rahoton Dail Mail.

Kara karanta wannan

Budurwa ta gurfanar da tsohon saurayinta a gaban kotun musulunci a jihar Kaduna

Bata sha kwayar Folic Acid ba

Mahaifar mai suna Caroline, mai shekaru 50 yanzu ta ce lokacin da ta tuntubi Likitar a 2001 kuma sukayi magana kan Folic Acid, bata fada mata shan maganin zai hana jaririyarta kamuwa da cutar spina bifida ba.

Yarinya tace da Likita Mitchell ta fadawa mahaifiyarta akwai yiwuwan jaririyar ta kamu da cutar, da bata dauki ciki a lokacin ba, rahoton Hindustan Times.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Budurwa ta shigar da Likitan da tayi karbi haihuwarta kotu
Da baki bari an haifeni ba: Budurwa ta shigar da Likitan da tayi karbi haihuwarta kotu Hoto: Daily Mail
Asali: UGC

Likitar ta kare kanta

Likitar, Dr Mitchell, ta musanta zargin da suke mata inda tace ta baiwa mahaifar Evie Toombes shawara sosai kafin ta haihu.

Lauyar budurwa, Susan Rodway, ta bayyana cewa da likitar ta bada shawara yadda ya kamata, da yanzu yarinyar ba tada nakasa.

Bayan haihuwar Evie Toombes a 2001, an same ta da cutar lipomylomeningocoele, mai nakasa gadon baya gaba daya.

Kara karanta wannan

Patience Jonathan ta rerawa mijinta waka mai ban dariya yayin da ya cika shekaru 64

Yarinyar ta bukaci Likitar ta biyata miliyoyin daloli.

Wani saurayi da ya kori budurwa saboda ba tayi kama da hotunan Istagram ba

Soyayyar wasu masu amfani da kafar sada zumunta ta rushe tun kafin a fara bayan saurayin ya kori budurwar daga ɗakinsa a haɗuwar farko.

Mutumin ya sallami matar daga ɗakin ne saboda ganin ta ba tare da wasu abubuwa da ya saba gani a hotunanta na Instagram ba.

A kokarin kare kanta, budurwan wacce ta amince da laifinta, ta yi wa mutumin bayanin cewa girman bayanta a haka ma ai ya yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel