Da Ɗumi-Ɗumi: NCDC ta tabbatar da ɓullar nau'in cutar korona na Omicron a Najeriya

Da Ɗumi-Ɗumi: NCDC ta tabbatar da ɓullar nau'in cutar korona na Omicron a Najeriya

  • Mahukunta a Najeriya sun ce sun gano sabon nau'in korona na Omicron a jikin mutum biyu a kasar
  • Hukumar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa, NCDC, ne ta sanar da hakan tare da bata tabbacin cewa ta fara bincike da bibbiya
  • Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta saka nau'in na Omicron cikin jerin cututtuka da ake yi wa kallon 'abin damuwa'

Abuja - Hukumar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa a Najeriya, NCDC ta tabbatar da bullar nau'in cutar korona na Omicron da ke firgita kasashen duniya.

Hukumar ta ce an gano mutane biyu da ke dauke da nau'in cutar a halin yanzu.

Dr Ifedayo Adetifa, Direkta Janar na hukumar ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannunsa.

Da Ɗumi-Ɗumi: NCDC ta tabbatar da ɓullar nau'in cutar korona na Omicron a Najeriya
Adetifa ya ce an fara binciken gano wadanda suka yi cudanya da masu dauke da cutar. Hoto: NCDC
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

NCDC ta ce an gano nau'in cutar biyu ne ta hanyar amfani da fasahar gano tsarin kwayar halita ta 'genomic sequencing'.

Wani sashi na sanarwar ya ce:

"Bisa tsarin yi wa matafiya na kasa da kasa gwaji, gwajin da aka yi a dakin gwaje-gwajen cututtuka na Abuja ta hanyar fasahar genomic sequencing ya tabbatar da bullar nau'in korona na Omicron a Najeriya."

NCDC din ta ce mutanen biyu da ke dauke da kwayar cutar ba su fara nuna alamun rashin lafiya ba kuma ta fara bincike don gano mutanen da suka yi cudanya da su.

Omicron: Muna sa ido kan lamarin, In Ji NCDC

A baya, hukumar ta NCDC ta bayyana cewa babu bullar nau'in cutar korona na Omicron a kasar a ranar Litinin 29 ga watan Nuwamba.

Hakazalika, NCDC ta sanar da cewa Ma'aikatar Lafiya ta Kasa ne da ke alhakin sa ido kan abin da ake ciki game da cutar.

Hukumar ta kuma bayyana cewa sabon nau'in na Omicron yana da saurin yaduwa, amma ta kara da cewa kawo yanzu, babu hujja da ke tabbatar da ikirarin cewa baya jin rigakafin da ake da su.

Hakan na zuwa ne bayan kasar Canada ta ce ta gano nau'in cutar a jikin wasu 'yan Najeriya biyu da suka tafi kasar ta.

Ku dakaci karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Online view pixel