Bidiyon wani mai yawon bude ido a garin da mutane ke wanke fuskokinsu da zinare ya karade kafafen sada zumunta

Bidiyon wani mai yawon bude ido a garin da mutane ke wanke fuskokinsu da zinare ya karade kafafen sada zumunta

  • Wani mai yawon bude ido, Joe Hattab, ya shayar da ma’abota amfani da kafafen sada zumunta mamaki bayan ya wallafa bidiyonsa a wani fitaccen gari da ke kasar Japan
  • A cikin garin akwai zinare mai tarin yawa wanda su suke sayar wa da kusan yawancin kasashen da ke nahiyar Asiya zinaren saboda tsabar yawansa a garin
  • Joe ya wanke fuskarsa da zinare maimakon ruwa kuma ya sha shayin zinare, har ila yau ya nuna yadda zinare ya ke lullube da alawa mai kankara ta Ice Cream

Japan - Yayin da wasu suke ganin zinare a matsayin ma’adani mai kimar gaske da tsada, garin Kanazawa ba su dauke shi a matsayin wani kayan gabas ba.

Wani mai yawon bude idanu, Joe Hattabya ya gano hakan bayan ya kai ziyara wani gari da ke Japan.

Kara karanta wannan

Matashi ya ziyarci birnin zinari inda mutane ke wanke fuska da shi, bidiyo da hotunan sun gigita jama'a

Bidiyon wani mai yawon bude ido a garin da mutane ke wanke fuskokinsu da zinare ya karade kafafen sada zumunta
Bidiyon mai yawan bude ido a garin da ake komai da zinare. Hoto: Joe Hattab
Asali: Instagram

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Joe, a wani bidiyo da ya wallafa a Facebook, ya nuna wasu yankuna da ke cikin kasar mai arziki da mutanenta.

Su na zuba zinare a kusan komai

Mutanen Kanazawa su na da arzikin zinare saboda haka su ke sa shi a cikin komai. Garin ne ke samar da fiye da kaso 90% na zinare ga kasar Japan, har sa shi suke yi cikin alawa mai kankara ta Ice Cream.

Joe ya yi mamaki akan yadda mutanen garin su ke shan Ice Cream da shayi wanda akwai zinare a cikinsa inda ya ce yana ganin akwai wata alfano tattare da shi.

Bidiyon wani mai yawon bude ido a garin da mutane ke wanke fuskokinsu da zinare ya karade kafafen sada zumunta
Mai yawon bude yana cin abinci a kwanon zinare. Hoto: Joe Hattab
Asali: Instagram

Wani ma’aikacin gidan abinci wanda ya mika wa mai yawon bude idon Ice Cream mai zinare ya bayyana cewa akwai yuwuwar kamuwa da cuta ta kaso 0.0001% idan mutum ya ci abu mai dauke da zinare a cikinsa. Duk da dai zinaren ba ya da dandano.

Kara karanta wannan

Ango ya fashe da kuka yayin da Amaryarsa ta wanke masa kafafu a gaban ‘yan biki

Ga bidiyo a kasa:

Nan da nan jama’a su ka fara cece-kuce a karkashin bidiyon inda wata Aamie Xierah ta ce:

“Zinare zai iya cutar da lafiyarka. Ko kuwa?.. Ko da yake, kusan komai ma yana cutar da lafiya har ganyayyaki da ‘ya’yan itace su na da sinadarai a cikinsu.”

Sami Redcliffe ya ce:

“Wannan lamari da ban dariya yake. Ta ya za ayi mutum ya ci zinare, anya ba ya da illa a jikin mutum? Maimakon ciyar da yaran talakawa da suke yunkurin mutuwa da yunwa ku na nan ku na kashin zinare. Zaku iya amfani da shi ku gina wa talakawa gidaje.”

Shailendra Patil ta ce:

“Zinare na da amfani ga lafiyar mutum, idan ka ga magungunan indiyawa za ka gane akwai zinare ko kuma azurfa amma mara yawa don anfanar da lafiya.”

Khalid Hassan Raza ya ce:

“Burin mutum ba ya taba karewa in har bai dakatar da zuciyarsa daga bukatu ba. Maimakon kashin zinare, ga talakawa can su na fama da abinda za su ci cike da kunci.”

Kara karanta wannan

Bidiyon yaron da ya ɓoye cikin injin jirgin sama don tsananin son zuwa ƙasar waje, ƴan sanda sun kama shi

Shugaban wurin aiki ya ba na ƙasa da shi da ke tattaki zuwa wurin aiki kyautar mota

A baya, kun ji wani matashi, Walter, ya yi tattakain mil 20 a ranar sa ta farko ta zuwa wurin aiki. Motar sa ta samu matsala ana gobe zai fara zuwa aikin hakan ya sa ya yanke wannan shawarar.

Kafin safiyar, ya yi kokarin tuntubar abokan sa amma babu alamar zai samu tallafi saboda ya sanar da su a kurarren lokaci kamar yadda Understanding Compassion ta ruwaito.

Daga nan ne ya yanke shawarar fara tattaki tun karfe 12am don isa wurin aikin da wuri. Matashin bai bari rashin abin hawan ya dakatar da shi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel