Ango ya fashe da kuka yayin da Amaryarsa ta wanke masa kafafu a gaban ‘yan biki

Ango ya fashe da kuka yayin da Amaryarsa ta wanke masa kafafu a gaban ‘yan biki

  • A wani bidiyo da aka sa a shafin Instagram, anga amarya ta rike tafin kafar mai gidanta, ta na gurzawa
  • Mutane sun gagara gane hikimar da ta sa mace ta ke wankewa mijinta kafa a fili a ranar bikin aure
  • Jama’a su na ta maganganu, wasu su na ganin bai dace a sa amarya wannan aiki gaban mutane ba

A wannan zamani, ma’aurata su kan zo da sabon salo a wajen bikin aurensu. A wasu lokutan, su kadai za su iya yin bayanin hikimar abin da suka yi.

A wani bidiyo da yanzu yake yawo a shafukan sada zumunta, an ga wata amarya ta na wanke kafafun mijin da za ta aura, hakan ya jawo maganganu.

An daura bidiyon ne a shafin Instablog9ja na Instagram. Kamar yadda aka saba, mutane su na ta tofa albarkacin bakinsu da suka ga wannan bidiyo.

Kara karanta wannan

Bidiyon yaron da ya ɓoye cikin injin jirgin sama don tsananin son zuwa ƙasar waje, ƴan sanda sun kama shi

Duk da wannan amarya ta na dauke da rigar biki, an gan ta har kasa ta na gogewa angon na ta kafa.

Fara gurje masa kafa ke da wuya, sai wannan an go ya fashe da kuka a gaban jama’a. Legit.ng ta ce za a iya ganin mijin a bidiyo ya na goge fuskarsa.

Wani ya mikowa angon tsummar hankici, inda ya yi amfani da ita da hannu ya rika share hawaye.

Ango ya fashe da kuka
Amarya na goge kafar ango Hoto: @instablog9ja
Asali: UGC

Me jama'a su ke cewa?

Wasu cewa su ka yi amaryar ta wankewa mai gidanta kafa ne da nufin a goge masu tambarin yaudara, ana sa ran hakan ya sa ya zauna da ita kadai.

@adepejuruth_cateringservice yace:

Awwww. Ina taya ka murna Sarkin Samari. Ran ka ya dade, ba ka isa ka ci amana ba fa. Idan ba haka ba, a sa dutse, a gurje kafafun nan na ka.

Kara karanta wannan

'Dan sanda ya gano matarsa na faɗa wa samarinta bata da aure, ya faɗa wa kotu shima ya haƙura da ita

@zaddyeleniyan ya rubuta:

"Ta na goge kafafunsa ne domin ta na hana shi cin amana da neman mata, mata mai hikima.”

@afrikannavy cewa tayi:

“Ba cikin kayan aure na ba, wani irin shirme kenan. A daki za ayi wannan.”
“Na taba ganin miji ya na yi wa matarsa wannan a ranar aure. Babu matsala, duk ba zan yi, ko in ce mata ta tayi mani ba.” - @solomon_buchi

Na yi rashin mahaifi - Zainab Ja’afar Adam

A wata hira da aka yi da ita, Zainab Ja’afar Adam tace har yau idan ta tuna da mahaifinta, Sheikh Ja’afar Mahmud Adam, ta na shiga daki ta yi kuka.

Marigayi Ja’afar Adam ya shaku da babban ‘diyarsa sosai, tace sun hadu karshe ne a garin Madina a lokacin da Shehin malamin ya zo yin umarah.

Asali: Legit.ng

Online view pixel