Kare ya zama babban Attajiri bayan ya gaji biliyan 205.4bn,Yana shirin siyar da katafaren gida kan 13m

Kare ya zama babban Attajiri bayan ya gaji biliyan 205.4bn,Yana shirin siyar da katafaren gida kan 13m

  • Wani kare, Gunther VI, da ya mallaki dala miliyan $500m (N205,420,000,000) a matsayin gado, yana shirin siyar da katafaren gidansa na alfarma
  • Karen na ɗaya daga cikin zuri'ar Gunther III, wanda ya gaji dumbin dukiya daga mamallakinsa, Karlotta Liebenstein, wanda ya mutu a 1992
  • Daga cikin dukiyar da karen ya gada akwai wani babban gini Tuscan a Italiya, wanda yake rayuwa a ciki

Wani kare a ƙasar Germany, Gunther VI, ya zama babban biliyoniya bayan an damka masa gadonsa na miliyoyin daloli.

An yi kiyasin cewa karen ya zama mamallakin dala miliyan $500m, kimanin biliyan N205,420,000,000, kuma yana rayuwa a wani katafaren gida, kamar yadda Dailystar ta ruwaito.

Gunther VI
Kare ya zama babban Attajiri bayan ya gaji biliyan 205.4bn,Yana shirin siyar da katafaren gida kan 13m Hoto: @dailystar
Asali: Instagram

Yadda lamarin ya faru

Gunther VI na ɗaya daga cikin zuri'ar Gunther III wanda ya taki sa'a ya gaji dumbin arziki daga uban gidansa, Karlotta Liebenstein, wanda ya mutu a 1992.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta fara rabawa talakawa kudi N1.6bn a jihar Jigawa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kakan kare Gunther VI ya gaji dukiyar ne shekaru 30 da suka gabata bayan ya cika burin uban gidan nasa, kamar yadda Business Journals ta rahoto.

Ta ya dukiyar ta kawo wannan lokacin?

Na tsawon wannan shekarun, akwai tawagar masu kula da dukiyar domin tabbatar da cewa jinin kare Gunther ne kaɗai suka amfana da ita.

Daya daga cikin amfanin da akai da dukiyar shine siyan wani katafaren gida, wanda a yanzun aka saka shi a kasuwa kan kudi $31.75 miliyan (N13,044,170,000).

Wannan gida da aka ɗaga za'a siyar ba shine asalin gidan da karen ke rayuwa ba, domin shi wancan yana Italiya.

Legit.ng Hausa ta tattaro muku ra'ayoyin mutane kan wannan labarin.

stanblewitt_ yace:

"Idan zaku buga labarin da zai ja hankalin mutane kamata ya yi ku yi akan wani abu da zai iya faruwa."

Kara karanta wannan

Da duminsa: Kotu ta garkame dalibin jami'a da ya yiwa Lakcara dukan kawo wuka

clojhughes90 yace:

"Kamata ya yi ace duk wani kare haka yake rayuwa."

A wani labarin kuma Basarake ya gwangwaje diyarsa da kyautar mota bayan ta kammala digiri da daraja ta farko

Diyar Sarkin, Gimbiya Zainab Adebunmi Adeyemi, ta kammala karatun digiri da sakamako mafi girma, ta samu kyautar mota.

Hotunan motar da suka watsu a kafafen sada zumunta ya jawo cece-kuce daga bakin mutane.

Asali: Legit.ng

Online view pixel