Gwamnatin China ta fadawa mutanenta su tsere, su bar Najeriya, Kongo da inda babu zaman lafiya

Gwamnatin China ta fadawa mutanenta su tsere, su bar Najeriya, Kongo da inda babu zaman lafiya

  • Ma’aikatar kasar wajen Sin ta kara jan kunnen mutanenta da ke kasashen da ake da matsalar tsaro
  • Gwamnatin Sin ta na so Sinawa su fice daga duk wuraren da ake da barazanar rashin tsaro a Afrika
  • Kakakin ma’ikatatar, Zhao Lijian ya bada sanarwa bayan hare-haren da aka kai a Najeriya da Kongo

Beijing - Ma’aikatar harkokin kasar wajen Sin da ke babban birnin Beijing, ya yi kira ga Sinawan da ke aiki a wurare masu hadari, su bar kasashen Afrika.

Jaridar Daily Trust tace mai magana da bakin ma’aikatar harkokin kasar wajen Sin, Zhao Lijian ya tabbatar da labarin sace wasu Sinawa a kasar Kongo.

Mista Zhao Lijian yace wasu mutane da ba a san su ba, sun dauke Sinawa biyar da ke aikin hako ma’adanai a kauyen Mukera da ke gabashin kasar Afrikar.

Kara karanta wannan

Rahoto: Yadda aka hallaka mutane 52 a Sokoto cikin kwanaki biyu kacal

Lijian yace an kashe wani jami’in tsaro daya yayin da ake yunkurin dauke wadannan Bayin Allah.

Har ila yau, Lijian ya tabbatar da aukuwar irin wannan lamari a Najeriya, inda ‘yan fashin daji suka yi garkuwa da wasu Sinawa uku a wani kamfani a Kogi.

Gwamnatin China
Shugaban kasar Sin Hoto: www.fmprc.gov.cn
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Gwamnatin Sin tace 'yan kasar ta su yi hattara

Rahoton yace kasar Sin ta kuma ja-kunnen mutanenta a kan shiga wuraren da ake fuskantar matsalar tsaro.

Jami’in kasar wajen yace akwai babbar barazanar tsaro a yankunan Najeriya da Kongo, kuma ba wannan ne karon farko da aka samu irin wannan matsala ba.

Kafin yanzu, Zhao Lijian yace gwamnati ta yi kira ga ‘yan kasarta su gujewa irin wadannan wurare. Najeriya na cikin inda barazanar ta fi kamari a yanzu.

Jawabin da Zhao Lijian ya fitar a Beijing

Kara karanta wannan

'Yan aware daga Kamaru sun shigo Najeriya, sun kashe mutane, sun kone gidaje

“Tun farkon shekarar nan, ake garkuwa da mutanen Sin a kasashen DRC da Najeriya bini-bini, hakan ya na kara jawo barazanar rashin tsaro.”
“Yanzu haka za mu kara gargadin ‘yan kasuwa da mutanen Sin da ke zuwa kasashen ketare, su yi hattara da duk wasu wuraren da ake da matsala.”
“Ga wadanda suke inda ake da matsala, su canza wurin zama ko su bar wurin cikin gaggawa.” – Lijian.

A baya an ji gamayyar kungiyoyin Arewa (CNG) ta soki bukatar shugabannin Ibo na neman shugaba Muhammadu Buhari ya bada umarni a fito da Nnamdi Kanu

Kakakin CNG, Abdul-Azeez Suleiman a wata hira da ya yi da manema labarai yace shugabannin su na yunkurin sa ayi watsi da doka wajen sakin shugaban na IPOB.

Asali: Legit.ng

Online view pixel