Buhari: 'Yan Najeriya suna gogayya a kasashen waje saboda ingantaccen ilimin da suke samu kafin su fita

Buhari: 'Yan Najeriya suna gogayya a kasashen waje saboda ingantaccen ilimin da suke samu kafin su fita

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce yanayin gasar da ‘yan Najeriya su ke yi a kasashen waje, alama ce ta ingantaccen ilimin da su ke samu a Najeriya kafin su fita daga kasar
  • Ya bukaci ‘yan Najeriyan da su ke riskar kawunansu a kasashen waje su yi kokarin ganin sun kiyaye dokokin kasheshen
  • Shugaban kasan ya yi wannan furucin ne yayin taro da karamin ministan harkokin kasashen waje na daular larabawa, UAE Shaikh Shakboot Alnahyan a ranar Juma’a

Faransa - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gasar da ‘yan Najeriya suke yi a kasashen waje alama ce ta ingantaccen ilimin da suke samu kafin su bar kasar, jaridar The Punch ta ruwaito.

Sakamakon hakan ya sa ya bukaci ‘yan Najeriya da su yi kokarin kiyaye dokokin kasashen da su ke zama.

Read also

Gumi ya caccaki 'yan aware: Igboho da Kanu ne suka kunna wutar rikicin Fulani a kudu

Buhari: 'Yan Najeriya suna gogayya a kasashen waje saboda ingantaccen ilimin da suke samu kafin su fita
'Yan Najeriya suna gogayya a kasashen waje saboda ingantaccen ilimin da suke samu kafin su fita, Buhari. Hoto: The Punch
Source: Facebook

Shugaban kasan ya fadi hakan ne yayin taro da karamin ministan harkokin kasashen waje na daular larabawa, Shaikh Shakboot Alnahyan, a Paris ranar Juma’a.

Mai ba shugaban kasan shawarwari na musamman akan harkokin yada labarai, Femin Adesina ne ya bayyana hakan a wata takarda mai taken ‘Gasar ‘yan Najeriya a ciki da wajen kasar, Shugaba Buhari ga ministan UAE.’

Buhari ya ce ‘yan Najeriya sun karade duniya

Adesina ya yanko inda Buhari ya ke cewa:

“Yan Najeriya su na nan ko ina, kuma su na ta gasa. Kuma gasar a gida take farawa inda su ke samun ingantaccen ilimi sai su koma kasuwanci daga nan kuma su zarce kasashen waje.”
“Shugaban kasa ya shawarci ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje da su kiyaye kansu daga karya dokokin kasashen da suke aiki ko kuma sana’o’i.”

Read also

‘Yan Sanda za su biya N50m ga iyalin wani Bawan Allah da dakarun SARS suka kashe da zalunci

Ya amince da bukatar UAE ta hada kai da Najeriya a bangarorin harkokin tattalin arziki, noma, masana’antu da samar da riga-kafin annobar COVID-19.

A bangaren minista Alnahyan, ya ce kasar sa tana matukar yabon mulkin shugaba Muhammadu Buhari, saboda jajircewarsa wurin ciyar da kasar gaba.

Abin da yasa har yanzu Nigeria bata zama ƙasaitacciyar ƙasa ba, Ministan Buhari

A wani labarin daban, Ministan Kimiyya da Fasaha, Ogbonnaya Onu, ya ce har yanzu Nigeria bata cimma babban matakin da ake sa ran ta kai ba a lokacin samun 'yanci saboda an yi watsi da irin halayen mazajen jiya da suka kafa kasar.

Ya yi wannan jawabi ne a babban birnin tarayya Abuja wurin wani taro da kungiyar 'Yan Kabilar Igbo ta shirya don karrama Rear Admiral Godwin Kanu Ndubuisi (mai ritaya), Daily Trust ta ruwaito.

Onu ya ce ya zama dole 'yan Nigeria su zama masu gaskiya, aiki tukuru da riko da halaye na gari idan suna son ganin kasar ta zama tauraro tsakanin sauran kasashe.

Read also

Kungiya tana so kotu ta hana Buhari kashe N26bn a kan abinci da zirga-zirga a 2022

Source: Legit.ng

Online view pixel