Bayan fargabar rashin lafiya, Sarauniyar Ingila mai shekara 95 ta ce babu wanda zai dawwama a duniya

Bayan fargabar rashin lafiya, Sarauniyar Ingila mai shekara 95 ta ce babu wanda zai dawwama a duniya

  • Sarauniya Elizabeth II ta Ingila ta ce babu wanda zai rayu har abada, ta bukaci shugabannin duniya da su bar batun siyasa a halin yanzu, su jajirce wurin shugabanci na kwarai
  • Bayan likitoci sun shawarci sarauniyar mai shekaru 95 da ta dakata da tafiye-tafiye saboda rashin lafiyar ta, ta yi wannan furucin a wani taron COP26
  • Ta shawarci shugabbannin da su ka halarci taron da su samar da ci gaba a duniya sannan ta yabi marigayin mijin ta, Yarima Philip wanda sai da su ka yi fiye da shekaru 70 da aure sannan ya rasu

Ingila - Sarauniya Elizabeth II, basarakiyar Ingila ta ce babu wanda zai yi rayuwa ta har abada, don haka ta shawarci shugabanni da su cire batun siyasa su yi mulki mai kyau, bisa ruwayar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Mayakan ISWAP sun yi awon gaba da fasinjoji 5 kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu

Sarauniyar mai shekaru 95, bayan shawarwarin likitoci akan ta dakatar da tafiye-tafiye saboda rashin lafiyar ta, ta yi wannan furucin ne ta bidiyo wanda aka gabatar a wani taro na COP26.

Bayan fargabar rashin lafiya, Sarauniyar Ingila mai shekara 95 ta ce babu wanda zai dawwama a duniya
Sarauniyar Ingila mai shekara 95 ta ce babu wanda zai dawwama a duniya. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jaridar Daily Trust ta ruwaito yadda sarauniyar ta yi kira ga shugabannin da su ka halarci taron da su samar da ci gaba mai kyau a duniya.

Sannan ta yabi marigayi Yarima Philip, mijin ta.

Kamar yadda ta ce:

“Abin alfahari ne a gare ni da nake jagorantar abubuwan da miji na ya yi a baya don taimaka wa mutanen duniyar nan ta hanyar ayyukan babban dan mu, Charles da babban dan sa, Williams. Ina matukar alfahari da su.”

Mijin ta ya rasu a watan Afirilun shekarar nan

Kowa ya ji radadin mutuwar mijin sarauniyar a watan Afirilu, lokacin ya na da shekaru 99, kuma sun kwashe shekaru 70 da aure tare da Sarauniyar.

Kara karanta wannan

Bayan lafawar tawagar Gana a Benue, wasu muggan makasa sun fito da sabon salon kisa

A cikin bidiyon, Sarauniyar ta kara da cewa ta na samun natsuwa sannan ta na sha’awar mutane ma su jajircewa komin shekarun su, musamman ma su karancin shekaru.

Ta shawarci kowa da ya yi na shi kokarin don samar da ci gaba a duniya.

Kazalika an hangi sarauniyar tana tuka wata mota kirar jaguar mai launin kore.

An gan ta sanye da kallabi da tabarau mai duhu, karo na farko da aka gan ta tun bayan kwanciya asibitin da ta yi sakamakon rashin lafiyar ta.

Bayan rayuwa cikin daji yana cin ciyawa, yanzu wankan sutturu na alfarma ya ke yi, ana girmama shi a gari

A wani rahoton, wani matashi, Nsanzimana Elie ya kasance a baya ya na zama cikin daji saboda yanayin suffar sa, sannan mutanen kauyen sa har tonon sa su ke yi.

Akwai wadanda su ke kiran sa da biri, ashe daukaka ta na nan biye da shi, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ba ni da hannu a dirar mikiya da jami'an tsaro suka yi a gidan Mary Odili, Malami

Mahaifiyar Elie ta ce Ubangiji ya amshi addu’ar ta na ba ta shi da ya yi bayan yaran ta 5 duk sun rasu, kuma ba ta kunyar nuna shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel