Jami’an tsaro a Faransa sun bindige wani mutum bayan tunkaro su da wuƙa ya na faɗin ‘Allahu Akbar’

Jami’an tsaro a Faransa sun bindige wani mutum bayan tunkaro su da wuƙa ya na faɗin ‘Allahu Akbar’

  • Jami’an tsaron wata tashar jirgin kasa da ke kasar Faransa sun harbi wani mutum a kirji har sau 2 sakamakon tunkaro su da wuka da ya yi ya na fadin ‘Allahu Akbar’
  • Dama sun dakatar da shi ne bisa karya dokar kasar ta kin sa takunkumin fuska da ya yi, wanda hakan ya harzuka shi, cikin fushi ya zaro zabgegiyar wukar sa
  • Bayan dauke shi da bindiga, ya na fadi kasa aka zarce da shi asibiti don yi ma sa taimakon gaggawa don yanzu haka ya na kwance rai a hannun Allah likitoci su na kokari akan sa

Faransa - ‘Yan sanda a kasar Faransa sun harbe wani mutum bayan ya zaro wuka tare da tunkaro su ya na kabbara da karfi sannan ya na fadin ‘kasar Faransa ta musulmai ce’.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Kotu ta hana Secondus dakatar da gangamin taron PDP na ƙasa

Kamar yadda Jaridar Standard ta ruwaito, lamarin ya faru ne a wata tashar jirgin kasa a daren ranar Litinin, 1 ga watan Nuwamba.

Jami’an tsaro a Faransa sun bindige wani mutum bayan tunkaro su da wuƙa ya na faɗin ‘Allahu Akbar’
Yan sanda a Faransa sun bindige wani mutum bayan tunkaro su da wuƙa ya na faɗin ‘Allahu Akbar’. Hoto: Evening Standard
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Jaridar Standard ta bayyana yadda mutumin ya samu miyagun raunuka bayan ya bayyana makamin sa ya na yunkurin daba wa jami’in tsaro a tashar jirgin kasa ta Saint-Lazare, daya daga cikin manyan tashoshin jiragen kasa da ke Faris.

Tushen lamarin

Da farko dai sun dakatar da shi ne saboda saba dokar kasar ta sa takunkumin fuska da ya yi.

Bayan haka ne ya zaro wukar sa tare da tunkuro jami’an tsaron ya na fadin 'Allahu Akbar' taken mayakan ISIS daga nan su ka harbe shi da bindiga a kirjin sa har sau 2.

Yanzu haka ya asibiti rai a hannun Allah.

Kamar yadda hukumar kamfanin jirgin kasar Faransa ta SNCF ta bayyana a wata takarda:

Kara karanta wannan

Kano: 'Yan Hisbah sun kama Aliyu Na Idris da ke son sayar da kansa kan N20m domin talauci

“Jami’an tsaro biyu su ka yi amfani da makaman su wurin kare kan su ta hanyar harbe shi.
“An wuce da shi asibiti don ya samu taimakon gaggawa.”

Takardun da aka gani a jikin sa su ka bayyana, an haifi mutumin a shekarar 1974 ne kuma dama ya taba samun wani sabani da ‘yan sanda sai dai jami’an binciken sirri ba su san da mutumin ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel