Da duminsa: Sojojin Sudan sun saka dokar ta baci, sun damke shugabannin farar hula

Da duminsa: Sojojin Sudan sun saka dokar ta baci, sun damke shugabannin farar hula

  • Rundunar sojin kasar Sudan ta hambarar da mulkin Firayim minista Abdallah Hamdok na kasar Sudan tare da kame shugabannin farar hula
  • Bayan haka, sojojin sun saka dokar ta baci a fadiin kasar sakamakon zanga-zanga da harbe-harbe da suka barke a birnin Khartoum na Sudan
  • US, UK, EU da UN sun yi Allah wadai da aukuwar lamarin duk da sojojin kasar sun dakatar da tashi ko saukar jiragen sama a kasar

Sudan - Rundunar sojin kasar Sudan ta hambarar da mulkin farar hula tare da saka dokar ta baci a fadin kasa baki daya.

Sojojin kasar sun kara da cafke shugabannin siyasa na kasa, Daily Trust ta wallafa.

Da duminsa: Sojojin Sudan sun saka dokar ta baci, sun damke shugabannin farar hula
Da duminsa: Sojojin Sudan sun saka dokar ta baci, sun damke shugabannin farar hula
Source: Original

Wannan na zuwa ne yayin da zanga-zanga mai tsanani ta mamaye babban birnin kasar Sudan, Khartoum.

Read also

Yanzu-Yanzu: Sojoji sun tsare Firayim ministan Sudan da wasu jiga-jigan gwamnatinsa

Dubban farar hula sun shiga zanga-zangar yayin da aka samu rahotannin harbe-harbe da ake ta yi, Daily Trust ta wallafa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hambarar da mulkin tsohon shugaban kasa, Omar Al-Bashir a shekaru biyu da suka gabata ya sa an kafa mulkin rikon kwarya wanda ya raba kan rundunar sojin da na farar hula a kasar.

Janar Abdel Fattah Burhan, wandda ke shugabantar majalisar hadin guiwa ta shugabannin farar hula, ya dora laifin kan 'yan siyasa.

Tsarin raba mulki wanda ya zamanto yarjejeniya tsakanin rundunar sojin kasa da kuma kungiyoyin gamayya na farar hula da ake kira da Forces for Freedom and Change (FFC) ne suka raba majalisar koli.

An shirya cewa za a yi mulkin shekara daya tare da shirya zaben kuma a koma mulkin farar hula.

Amma kuma wannan yarjejeniyar ta tashi inda aka samu kungiyoyin siyasa mabanbanta da kuma rabe-rabe a cikin rundunar sojin.

Read also

Jami’an DSS, ‘yan sanda, sojoji sun kewaye kotun Abuja a shari’ar Nnamdi Kanu

Firayim minista Abdallah Hamdok na daga cikin wadanda aka tsare tare da wasu mukarrabansa da sauran shugabannin farar hula.

Wakilin Ingila a Sudan da Sudan ta kudu, Robert Fairweather, ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa kamen da rundunar sojin kasar ta yi wa shugabannin farar hula "cin amana ne na juyin juya hali, karbar mulki da kuma cin amanar jama'ar Sudan".

Amurka, majalisar dinkin duniya, kungiyar gamayyar Turai da ta Larabawa sun bayyana damuwarsu kan aukuwar lamarin.

A halin yanzu an rufe filin sauka da tashin jiragen sama na Khartoum kuma an dakatar da tashin jirage zuwa wajen kasar.

Juyin mulkin ya na zuwa ne bayan wata daya da aka hambarar da gwamnatin shugaban kasa Alpha Conde na Guinea.

Sojoji sun tsare Firayim ministan Sudan da wasu jiga-jigan gwamnatinsa

A wani labari na daban, rahotanni masu girgiza zukatan da ke zuwa a halin yanzu shi ne na daurin talalan da sojojin kasar Sudan suka yi wa Firayin Ministan Abdallah Hamdok.

Read also

Kaduna: Sojin sama da na kasa sun ragargaji 'yan bindiga 50 a Birnin Gwari

Kamar yadda Al-Jazeera ta wallafa, sojojin sun yi ram da Hamdok tare da wasu daga cikin ministocinsa a sa'o'in farko na ranar Litinin, 25 ga watan Oktoba.

Daga cikin jami'an gwamnatin Sudan da sojoji suka kama, akwai ministan masana'antu, Ibrahim Al-Sheikh, ministan yada labarai, Hamza Baloul da kuma mai bai wa Hamdok shawara kan yada labarai, faisal Mohammed Saleh.

Source: Legit

Online view pixel