Sani Hamza
5088 articles published since 01 Nuw 2023
5088 articles published since 01 Nuw 2023
Kwankwaso ya halarci taron tattalin arzikin daji a fadar shugaban kasa, inda aka jaddada amfani da fasaha wajen bunƙasa fannin daji da habaka tattalin arziki.
Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya ce ba zai amince da dukan mata ba, yana mai kira ga malamai da gwamnati su kawo karshen cin zarafin mata da ake yi a Kano.
Barista Kashim ya fice daga PDP yana mai nuna godiya ga jam’iyya da mazaba, inda ake hasashen zai sake yin takarar gwamna a 2027 karkashin wata sabuwar jam’iyya.
Dr. Akinola ya ce asibitin ABUAD na da ingantattun kayan aiki da ƙwararrun likitoci da za su iya ceton rayuwar Muhammadu Buhari da ace ya yi jinya a can.
A Indonesia, jirgin ruwa ya kama da wuta yayin da yake tafiya daga tsibirin Talaud zuwa Manado, an ceto mutum 568, uku sun mutu, ciki har da mace mai juna biyu.
NDLEA ta cafke shugaban dillalan kwayoyi Okpara Chigozie tare da gano hodar iblis, methamphetamine a mota da gidansa. An kuma kama Tramadol da Rohypnol a Legas.
Masu zuba jari daga kasar China sun gamsu da albarkatun yankin Rabba da ke jihar Neja, kuma gwamnati ta sha alwashin samar da yanayin kasuwanci mai sauki gare su.
Matashi Kelvin Ubakpororo ya amsa laifin kashe budurwarsa a Sapele saboda rikicin da suka yi. Ya bayyana cewa ba ya cikin hayyacinsa lokacin da ya aikata kisan.
Jam’iyyar ADC ta ce Tinubu ya gaza cika alkawarin samar da wutar lantarki ta awanni 24 ga 'yan Najeriya, inda ta ce miliyoyin mutane na ci gaba da rayuwa cikin duhu.
Sani Hamza
Samu kari