Sani Hamza
5072 articles published since 01 Nuw 2023
5072 articles published since 01 Nuw 2023
Wani Sarki a jihar Osun, Oba Clement Adesuyi Haastrup Ajimoko III, da ke sarautar Ijesa, ya tsige basarake, Busuyi Gbadamosi, bisa zargin satar injunan wuta.
Ana zargin yan ta'addan Lakurawa sun hallaka wata mata mai suna Mai-Kudi Danginjo da aka ce ta kai shakaru 45 a jihar Sokoto kan zargin maita da ake yi mata.
Tsohon hadimin shugaban kasa a Najeriya, Reno Omokri ya karyata zargin wani mai gabatar da shirye-shirye na Amurka, Bill Maher cewa ana kashe Kiristoci a Najeriya.
Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya yi sauye-sauye a majalisar zartarwa wanda ya raba kwamishinar mata da ci gaba yara, Zainab Baban-Takko da mukaminta.
Kungiyar PENGASSAN ta ce zaman lafiya zai dawo, kuma za ta ci gaba da raba mai idan matatar Dangote ta maido da ma’aikata 800 da ta sallama kwanan nan.
Kungiyar ma’aikatan man fetur, PENGASSAN, ta rufe matatar man Dangote tare da ayyana yajin aikin kasa baki daya bayan sallamar ma’aikata 800 ƴan Najeriya.
Gwamnatin tarayya ta karyata ikirarin kisan kiyashi a Najeriya, ta ce ’yan ta’adda suna kai hari ga Musulmi da Kiristoci ba tare da bambancin addini ba.
Shugaban Izala reshen Kaduna, Sheikh Bala Lau, ya yabawa hukumar tsaro ta farin kaya, DSS kan abin da ke faruwa game da Sheikh Abubakar Shu'aibu Lawan Triumph.
Fitacciyar mai bin addinin gargajiya, Yeye Osunfunmilayo Ajile, ta ce ba za ta bar asalin addinin gargajiya ba duk da barazanar malaman Musulunci a Kwara.
Sani Hamza
Samu kari