Muhammad Malumfashi
19605 articles published since 15 Yun 2016
19605 articles published since 15 Yun 2016
Sabon Gwamnan Kano ya nada SSG, PPS da COS a ranar farko. An canza Shugabannin hukumar da ke kula da jin dadi da walwalar alhazan jihar Kano a ranar Litinin.
Abba Kabir Yusuf wanda ya fi shahara da Dadiyata, ya yi alkawarin yin bincike a game da bacewar Malam Abubakar Idris (Dadiyata)a matsayinsa na Gwamnan Kano.
Bola Tinubu ya zama shugaban kasa a shekaru 71, mai dakinsa ta ce tana shirin cika shekara 63, Remi Tinubu ta tabo batun mulkin Najeriya a karkashin mai gidanta
Mun tattaro abubuwan Bola Tinubu ya fada a wajen rantsar da shi. Shugaban ya kawo maganar tallafin fetur, ayyukan yi, tsaro, ya dage sosai a kan sha’anin matasa
Dr. Dikko Umaru Radda ya fitar da mukaman farko. Arch. Ahmed Musa Dangiwa ya zama SSG, Jabiru Tsauri da Barr. Muhtar Aliyu Saulawa sun zama shugabannin fadar
Kafin Muhammadu Buhari ya bar ofis, ya nada sababbin Darektoci a tashar talabijin na NTA. A yayin da aka sanar da nadin, Bola Tinubu ya karbi mulkin Najeriya.
Farashin man fetur ya fara lulawa sama tun kafin Bola Ahmed Tinubu ya gano kujerarsa a Aso Rock, hakan ya yi sanadiyyar a daina saida mai a kan N195 zuwa N210.
A yau Litinin 29 ga watan Mayu ne aka fatan rantsar da zababben shugaban kasa Bola Tinubu. An shirya yin bikin ne a Eagle Square, Abuja misalin karfe 10 na safe
Za a ji labari Gwamnan jihar Kano mai barin gado, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya gamu da cikas a bukin rantsar da sabon shugaban kasa a Eagle Square da ke Abuja.
Muhammad Malumfashi
Samu kari