Jami’an Tsaro Sun Takawa Ganduje da Mai Dakinsa Burki a Wajen Rantsar da Tinubu

Jami’an Tsaro Sun Takawa Ganduje da Mai Dakinsa Burki a Wajen Rantsar da Tinubu

  • Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya na cikin wadanda su ka halarci bikin rantsar da Bola Tinubu
  • Tsohon Gwamnan bai samu yadda ya so ba domin an hana shi da matarsa zama da manyan baki
  • Ganduje ya yi gaggawar barin Kano inda ya kamata ya mika mulki saboda ya halarci rantsuwar

Abuja - Duk da Abdullahi Umar Ganduje ya yi sammakon barin garin Kano domin halartar bikin rantsar da Bola Tinubu, hakan ya zo da matsala.

Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya isa filin Eagle Squre inda ake bikin rantsar da sabon shugaban Najeriya a garin Abuja, amma sai ya gamu da cikas.

BBC Hausa ta ce tsohon Gwamnan na Kano ya samu matsala ne yayin da ya nufi shiga sashen da ake ajiye manyan baki watau VIP a farfajiyar.

Kara karanta wannan

Tinubu: ‘Dan takaran LP, Peter Obi ya yi maganar ‘shirin’ zanga-zanga a Eagle Square

Abdullahi Ganduje
Abdullahi Ganduje a lokacin ya na mulki Hoto: @aabaji1
Asali: Facebook

Ba ku isa ba!

A nan jami’an tsaro su ka nunawa Abdullahi Ganduje da mai dakinsa watau Hafsah Ganduje da su ke tare cewa ba su da hurumin shiga sashen.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Masu kula da bikin sun ankarar da tsohon Gwamnan cewa baki masu alfarma kadai su ke iya kai wa ga wannan wuri, wanda su ba su a cikinsu.

Kamar yadda rahoton ya nuna, Ganduje da uwargidarsa su na dauke ne da koriyar takardar gayyata wanda ta ke ba mutum gama-garin kujera.

Wadanda ake bari su shiga sashen VIP su na dauke ne da takardar gayyata mai launin gwal, sai mutum ya na da wannan zai iya zama a sashen.

Ganduje ya bar garin Kano ba tare da ya mika mulki ba, saboda taron na yau.

An kora Soludo

A dalilin haka ne jami’an tsaro su ka ki ba Mai girma Farfesa Charles Chukwuma Soludo irin wannan dama da ya nemi ya tsallake matsayinsa.

Kara karanta wannan

A banza: Peter Obi ya fadi abin da zai faru dashi bayan an rantsar da Tinubu

Duk da ya na Gwamna mai-ci a jihar Anambra kuma tsohon Gwamnan babban bankin CBN, Soludo bai da hurumin zama da baki masu alfarma.

Tinubu ya shiga Eagle Square

Rahotannin da mu ke kawo sun tabbatar da cewa Bola Ahmed Tinubu ya isa filin Eagle Square kafin karfe 10:00 na safe inda za a rantsar da shi.

Da safiyar nan ne zababben shugaban kasar ya bar masaukinsa da ke 'Defense House' a Abuja tare da 'yan tawagarsa, daga nan zai wuce Aso Rock.

Asali: Legit.ng

Online view pixel