Ibrahim Yusuf
4362 articles published since 03 Afi 2024
4362 articles published since 03 Afi 2024
Jam'iyyun adawa a Najeriya na fama da rikicin cikin gida a Najeriya inda aka samu shugabbi har biyu a NNPP, ADC, SDP da LP masu ikirarin shugabanci.
Jagoran 'yan ta'adda, Bello Turji ya sanar da ajiye makamai bayan zaman sulhu da aka yi da shi a Zamfara. Sheikh Musa Yusuf Asadus-Sunnah ne ya sanar da haka.
Gwamnatin jihar Yobe za ta karrama dalibai mata biyu, Nafisa Abdullahi da Rukayya Muhammad Fema da suka fafata a gasar Turanci da aka yi a London.
Mutanen Zaar da ke karamar hukumar Tafawa Balewa a jihar Bauchi sun yi wa shugaba Bola Ahmed Tinubu alkwarin kuri'u a 2027 saboda ba Yakubu Dogara mukami.
Sabon rikici ya barke a jihar Filato tsakanin makiyaya 'yan kabilar Fulani da wasu mazauna karamar hukumar Bokkos. An kashe wata mata tare da kona gidaje.
Sheikh Isa Ali Pantami ya bukaci gwamnatin Najeriya karkashin Bola Tinubu ta karrama Nasifa Abdullahi Aminu da ta lashe gasar Turanci ta duniya a London.
Jam'iyyar APC ta gargadi 'yan Najeriya da cewa Atiku Abubakar, Nasir El-Rufa'i, Rotimi Ameachi da Peter Obi cewa za su rusa tsarin karba karba a siyasar Najeriya.
Mai martaba Khalifa Muhammadu Sanusi II ya ziyarci asibitin Murtala domin duba lafiyar wani masoyinsa, Sadiq Gentle da 'yan daba suka sassara a jihar Kano.
Balarabe Sarkin Kofar Kano ya tuba a gaban mai martaba Muhammadu Sanusi bayan ya dawo daga bangaren mai martaba Aminu Ado Bayero daga fadar Nasarawa
Ibrahim Yusuf
Samu kari