2019: Babu madadin shugaba Buhari - Minista

2019: Babu madadin shugaba Buhari - Minista

- Karamin ministan kwadago da diban ma’aikata, Farfesa Steohe Ocieni yace har yanzu babu madadin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a cikin yan takarar kujeran shugabancin kasa a zaben 2019

- Ministan ya bukaci yan Najeriya da kada su bari yan jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), su yaudare su

- Tsohuwar hadimar Sanata Rabiu Kwankwaso Balaraba Ibrahim Stegert, ta bar jam’iyyar PDP zuwa APC

Har yanzu Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ne dan takara mafi aminci a tsakanin yan takarar kujeran shugabancin kasa a zaben 2019, cewar karamin ministan kwadago da diban ma’aikata, Farfesa Steohe Ocieni.

Ya bayyana hakan ne a lokacin gangamin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Anyigba, Kogi, jaridar Guardian ta ruwaito.

Legit.ng ta tattaro cewa ministan ya bukaci yan Najeriya da kada su bari yan jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), su yaudare su, sannan ya kuma kaddamar da cewar babu madadin gwamnatin Gwamna Yahaya Bello.

2019: Babu madadin shugaba Buhari - Minista
2019: Babu madadin shugaba Buhari - Minista
Asali: Depositphotos

A halin da ake ciki, Balaraba Ibrahim Stegert, wata tsohuwar hadimar Rabiu Musa Kwankwaso ta bar jam’iyyar PDP a ranar Lahadi, 16 ga watan Disamba.

Yayinda ake gwagwarmayar siyasa a jihar Kano, Balaraba, babbar hadimar Kwankwaso ta saya sheka zuwa jam’iyyar APC.

KU KARANTA KUMA: 2019: Shugaba Buhari bai shirya ma zabe ba - PDP

Bayan gwamnatin Umar Ganduje ta bar mata matsayinta na bai ma gwamna shawara akan ma’adinai, Balaraba tayi murab us ta sake hadewa da ubangidanta (Kwankwaso) a PDP a shekarar 2017.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel